Jarumin finafinan Bollywood Dharam ya ragamu gidan gaskiya
Fitaccen jarumin finafinan masana'antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya.
Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da "ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya."
Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da "mutum mai sauƙin kai" ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya.
Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya fito a finafinai sama da 300 a gomman shekaru da ya yi a masana'antar.
An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1935 a ƙauyen Nasrali da ke lardin Punjab Ludhiana. Malaminsa a makaranta n...








