Wednesday, February 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta’addanci ba ne – FBI

Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta’addanci ba ne – FBI

Duk Labarai
Jami'ar hukumar tsaro ta FBI a Amurka, Alethea Duncan, ta ce ta karɓe ragamar bincike kan harin da wani direba ya kai wa masu bikin sabwar shekara a birnin New Orleans. Yayin jawabin da ta yi, ta ce "wannan ba harin ta'addanci ba ne", abin da ya saɓa da kalaman magajin garin. Zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa aka samu mabambantan bayanai ba game da lamarin da ya jawo mutuwar mutum 10. Duncan ta ce akwai yiwuwar wani abin fashewa da aka gano a wurin kuma ana binciken gano gaskiyar hakan. Ta ce mutane za su ƙaurace wa wurin "har sai mun gano abin da ke faruwa".
Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Duk Labarai
Kafofin yaɗa labarai a Nijar da Mali da Burkina Faso sun ruwaito a ranar Litinin cewa ƙasashen za su kafa wata tashar talabijin ta intanet da zimmar "ƙarfafa haɗin kai da kuma yaƙi da labaran ƙarya" a yankinsu na Sahel. Ƙasashen uku da sojoji ke mulki, sun kafa ƙawance da suka kira Alliance of Sahel States, wanda suke kira da Aes a Faransanci. "Ana sa ran tashar za ta inganta harkokin sadarwa tsakanin ƙasashen Sahel kuma a samu tasiri mai ɗorewa bisa muradin shugabannin ƙasashen biyu," in ji rahoton shafin Actu Niger. An ƙulla ƙawancen ne a 2023 bayan sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, wadda suka zarga da yi wa ƙasashen Yamma aiki. Nijar da Mali da Burkina duka sun yanke alaƙa da ƙasashen Yamma kamar Faransa...
Sojojin Najariya sun ce sun kashe ‘yan Bindiga 10,937 da kama guda 12,538 a shekarar 2024

Sojojin Najariya sun ce sun kashe ‘yan Bindiga 10,937 da kama guda 12,538 a shekarar 2024

Duk Labarai
Sojojin Najaria sun bayyana gagarumar nasarar da suka samu a shekarar 2024 inda suka ce sun kashe 'yan Bindiga guda 10,937 inda suka kama guda 12,538. Kakakin sojin Major General Edward Buba ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda yake bayani kan ayyukan da sojojin suka gudanar a shekarar 2024. Hakanan yace sojojin sun kubutar da jimullar mutane 7,063 da aka yi garkuwa dasu. Sannan aun kwace jimullar makamai 8,815 da Albarusai 228,004.
Ko an yi sulhu ba zamu daina yaki da kkashe mutanen Gaza ba>>Inji Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu

Ko an yi sulhu ba zamu daina yaki da kkashe mutanen Gaza ba>>Inji Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ko da an yi sulhu tsakaninsu da kungiyar Hamas wa'adin sulhun na karewa zasu ci gaba da yaki a Gaza. Yace suna fatan a yin sulhun amma ba zasu daina yaki ba har sai sun cimma muradinsu na yin yakin a Gaza. Masu shiga tsakani dai sun bayyana damuwa akan matsayin da Firaiministan Israel ya dauka. Israel na son cimma kawar da kungiyar Hamas a matsayin kungiya me rike da makamai ko kuma kungiyar siyasa, kwato duka wadanda aka yi garkuwa dasu da kuma hana Gaza zama barazana ga Israel nan gaba. Kungiyar Hamas dai ta ki amincewa ta saki mutanen da take gasrkuwa dasu su 100 inda itama ta gindaya sharudanta.
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Yayin Da Ahmed S. Nuhu Ke Cika Shekara 18 Da Rasuwa A Yau, Ita Kuma Mahaifiyasa Ta Rasu A Yau Din

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Yayin Da Ahmed S. Nuhu Ke Cika Shekara 18 Da Rasuwa A Yau, Ita Kuma Mahaifiyasa Ta Rasu A Yau Din

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} "A daidai ranar da abokinmu Marigayi Ahmed S Nuhu yake çıka shekaru 18 da komawa ga Mahaliccinmu, ita kuma mahaifiyarsa Allah Ya yı mata rasuwa. Inda za a yi jana’izarta a garin Jos kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Muna addu’ar Allah Ya jikan ta, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sa Aljanna Madaukakiya ce makomarta. Idan ta mu ta zo kuma Allah Ya sa mu çıka da kyau da İmanı" kamar yadda shugaban hukumar tace finafinai, Abba El-Mustapha ya wallafa.
Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Duk Labarai
Shugaban riko na Jam'iyyar PDP, Umar Damagum ya bayyana cewa, sune suka gogar da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso har ya zama abinda ya zama yanzu. Damagun ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da BBChausa. Yace koda duka jam'iyyun hamayya zasu hade ba zasu yi nasarar kwace mulki daga hannun APC ba tare da PDP ba. Kwankwaso a baya ya soki Jam'iyyar PDP inda ya bayyana irin rashin kyautawar da suka masa data sa ya fice daga cikin Jam'iyyar. Saidai Damagun yace duk da kalubalen da Jam'iyyar ta PDP ke fuskanta amma har yanzu tana nan da kwarjininta.
Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Duk Labarai
Wannan Zainab ce wadda kusan duk masu bibiyar kafafen sada zumunta sun santa. Diyace a wajen marigayi, sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wadda rayuwarta ke cikin damuwa da rashin tabbas. A sabon bidiyon da ta yi ta bayyana cewa gata karfe dayan dare a Birnin Legas tare da mahaifiyarta da kaninta wanda kuma akanta suka dogara. Tace mahaifinta ya barta ba ilimi ba wani abu da zata iya dogaro dashi, bata da aikin yi. Tace ta gaji bata san yadda zata yi ba, babu wanda ke taimakonta. A baya dai Gwamnatocin Ganduje dana Abba Gida-Gida sun taimaka mata. A wannan karin, Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad yayi kiran da a sake taimakawa Zainab, musamman Gwamnatin jihar Kano. Kalli Bidiyon anan

Yadda ake raka atanil fajr

Addu'a
FALALAR RAK'ATAYIL FAJR Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.Malamai sun ce ana karanta Fatiha ne da Qul Ya ayyuhal Kafirun, da kuma fatiha da Qul Huwal-Lahu acikinta. KUMA ana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIF...