Da Duminsa: Dokar Haraji tana nan zata fara aiki ranar 1 ga watan Janairu>>Inji Shugaba Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu gudu babu ja da baya.
Dokar Haraji tana nan za'a yi ta kamar yanda aka shirya watau nan da 1 ga watan Janairu.
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace Harajin zai kawo ci gaba a Najeriya sosai.








