Wannan wata fastuwa ce data dauki hankula a kafafen sada zumunta, da yawan matasa sun ce zasu koma zuwa cocinta.
https://twitter.com/i/status/2008557394910191910
Tsoho gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa dan Abba ya koma jam'iyyar APC bai ga wani abin Butulci ba.
Yace watakila Kwankwaso ya manta amma idan shi ya manta, mutane basu manta ba, yace shima Kwankwason ya canja jam'iyyu.
Yace tare suka shiga jam'iyyar NNPP da su Kwankwaso amma rashin Adalci wajan rabon mukamai yasa suka fita dsga jam'iyyar.
Yace yawanci dan siyasa na canja jam'iyya ne bayan ya ssmu goyon bayan mabiyansa dan haka bai ga abin ace Abba yawa wani Butulci ba.
Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
Kwanakin baya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, ana shirin yiwa Anthony Joshua hukuncin daurin rai da rai.
Direban dai shine ya tuka motar su Anthony Joshua da abokansa 2 wadda ta yo Khàdàry
Abokan Anthony Joshua 2 sun rasu a dalilin khadarin kuma Anthony Joshua ya ji ciwo.
Direban me suna Adeniyi Kayode dan kimanin shekaru 47 yana fuskantar hukuncin daurin rai da rai, hukumomin sun ce suna ci gaba da bincike akansa.
Bayan nasarar da suka yi akan Dr. Congo, An ga kasar 'yan Algeria suna ta tsalle da murnar cewa sun kai ga wasan Quarter finals.
Sun rika bayyana cewa, saura Najeriya.
https://twitter.com/i/status/2008667002882453854
An hango Tsohon dan wasa kuma tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane yana ta murna bayan da kasar Algeria ta kai ga wasan Quarter finals.
Dan Zinedine Zidane shine golan kungiyar kwallon Algeria kuma Zidane da matarsa tun da aka fara gasar cin kofin ta AFCON suka je kasar Morocco suke kallo.
https://twitter.com/i/status/2008659253498962132
Rahotanni sun ce an sace wasu Shanu da yawa, amma jami'an tsaro suka yi nasarar kwato su.
Da aka tara shanun a waje daya wani bafulatani ya je yace shima an sace masa, sai aka ce menene hujjarsa, sai yace zai kira saniyarsa ta zo.
Kuma yana kiranta sai ta zo inda yake.
https://twitter.com/i/status/2008560434354548960
Tauraron mawakin Arewa, Ali jita ya bayyana cewa, kaso 70 cikin 100 na 'yan Najeriya, Musulmai da Kiristoci duk cin hanci ya musu katutu.
Ya bayyana hakane a shafinsa na X.
Da yawa sun yadda dashi akan wannan maganar.
https://twitter.com/i/status/2008267136108728718
Wannan wata matace data bayyana cewa, ta daina zuwa coci saboda ta gano gaba daya raina musu hankali ake yi.
Tace ta gaji da dukawa wasu turawa da aka saka musu hotunansu a coci ana cewa wai Jesus ne da mahaifiyarsa., Mary.
Tace karyane basu bane.
Tace Turawa da a yanzu da yawansu ma basu yadda da addini ba, yawancinsu abinda suka ga dama kawai suke aikatawa shine za'a ce sune Jesus da Mary?
Ta bayyana cewa, Mijinta ya rika ce mata wai shedan yayi galaba akanta.
https://twitter.com/i/status/2008488324370157857
Wannan hoton ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda aka ga dan gidan Ministan Babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike akan kujera me Laushi amma shugaban jam'iyyar APC na jihar Rivers akan kujera me tauri ya dauki hankula.
An dauki hotonne lokacin da Wike ya kai ziyara jiharsa ta Rivers.
Da yawa dai na ganin hakan bai dace ba.
https://twitter.com/i/status/2008780577835807078