Tsageran IPOB dake son kafa kasar Biafra sun tarwatsa wani shingen sojoji dake kan titin Umuokpara - Onuimo.
https://twitter.com/kepukepunews/status/1856631618468766129?t=pKTYJCNAho4pEg4Ba6tcMA&s=19
An gansu suna harbi a iska da ture duk wani shinge da sojojin suka saka a wajan.
Dan jarida me binciken kwakwaf, Fisayo Soyombo ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shinkafa zuwa cikin Najeriya.
A bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce yanzu haka ana sauke shinkafar da aka shigo da ita daga kasar Benin Republic a Lusada dake karamar hukumar Ado Odo/Ota ta jihar Ogun.
Soyombo ya bayyana cewa lamarin na faruwane a ranar Laraba inda yace kuma an sallami duka wani jami'in Kwastam da zai kawo tangarda a lamarin.
Dan jaridar yace sauran shinkafar za'a tafi da ita zuwa Legas.
A baya dama dan jaridar ya bayar da bayanai akan shigowa da shinkafar amma hukumar kwastam ta karyatashi.
Mining din $Major na Telegram da suka dade ana tsammanin shiga kasuwarsu sun bayyana ranar 28 a matsayin ranar shiga kasuwa.
https://twitter.com/okx/status/1856638910786306426?t=JZdYSZuc0Cpheh8L-7hVRQ&s=19
OKX ne suka tabbatar da hakan a sanarwar da suka fitar yau.
OKX sun sanar da cewa da misalin karfe 12 UTC watau Misalin karfe 1 agogon Najeriya zasu shiga kasuwar.
Tun dai a watan October ne Major suka ce zasu shiga kasuwa amma hakan bai yiyu ba.
A yayin da aka shigar da wata kara a kotun kasar Amurka ake neman bayanai game da rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a baya inda ake zargin ya yi ta'ammuli da kwaya da kuma maganar ingancin takardun karatunsa, kasar Amurka tace ba zata bayar da wadannan bayanai ba.
Dan jarida, David Hundeyin ne ya shigar da kara yake neman bayanai akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kuma tun a shekarar data gabatane dai kotun kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanan da yake nema.
Dan jaridar yace hukumomin kasar Amurka, CIA, FBI, da DEA sun shigar da kara inda suma suke neman cewa kada a bashi bayanai akan shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu inda CIA wadda kungiyar leken Asiri ce ta kasar Amurka tace Bola Ahmad Tinubu wakilinta ne da take amfani dashi wajan cimma muradunta.
Zuwa yanzu dai...
Dankalin Hausa na da matukar amfani ga dukkan dan adam.
Amma a wannan rubutun zamu bayyana amfanin Dankalin Hausa ga mata.
Ga mata dake son rage kiba, idan aka rike cin dankalij Hausa, yana sanya rage kiba ba tare da illa ba.
Ga macen dake fama da bushewar gaba, cin dankalin Hausa yana kawo ruwan gaba ga mace ta yi ni'ima sosai.
Hakanan Dankalin Hausa yana taimakawa sosai wajan kara karfin gani kamar yanda masana suka tabbatar.
Hakanan ga me fama da hawan Jini, cin dankalin Haisa yana sanya jinin mutum ya tsaya a ma'auni madaidaici ba zai hau ba.
Ga masu neman haihuwa, Dankalin Hausa yana taimakawa sosai mace ta samu daukar ciki. Hakanan yana karawa kwayayen mace inganci wanda shima duk taimako ne wajan daukar ciki.
Ga matan da suka manyanta sosai har suka daina haihu...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya karbi mulkin Najeriya a yayin da take cikin wahalar rashin tabbas na tattalin arziki.
Shugaban yace shiyasa ya dauki matakai tsaurara musamman a bangaren kudi dan ganin ya kawo ci gaba.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan rantsar da zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo inda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilceshi.
Yace a yanzu saboda matakan da ya dauka, kasar ta dauki hanyar ci gaba da nasara.
Rahotanni sun nuna cewa mutane 243,000 sun daina biyan kudin DSTV da GoTV saboda tsada rayuwa.
Kamfanin wanda na kasar Afrika ta kudu ne ya bayyana cewa ya rasa wadannan mutanen ne daga watan Afrilu na wannan shekare zuwa watan Satumba na shekarar.
An ga hakanne a cikin bayanan yanda kamfanin ya gudanar da kasuwancinsa wanda ya fitar a karshen watan Satumba.
Kamfanin ya alakanta hakan da tsadar rayuwa wadda ta hana da tsadar kayan abinci, wutar lantarki, da man fetur.
Kamfanin ya kara da cewa, ya rasa mitane 566,000 a gaba dayan nahiyar Afrika wanda suka daina biyan kudin DSTV da GoTV din.
Babban fasto a cocin The Methodist Church of Nigeria, Rev. Emmanuel Udofia ya bayyana cewa akwai yunwa a Najeriya.
Dalilin hakane ma yasa ya jawo hankalin fastoci 'yan uwansa dasu rika karfafa gwiwar mutane.
Ya kuma baiwa fastocin shawarar yiwa mutane addu'a da basu shawarwari masu kyau.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja daga kasar Saudiyya inda ya je wajan taron kasashen Musulmai.
Jirgin na shugaba Tinubu ya sauka ne da misalin karfe 8 na darennan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International airport.
Manyan jami'an gwamnati ne suka mai maraba bayan saukarsa.
Tabbas Kanunfari yana maganin sanyi kamar yanda masana ilimin kiwon lafiya suka tabbatar.
A mafi yawancin lokuta akan hada Kanunfari da zuma ne dan samun sakamakon maganin sanyi me kyau.
Masana sun bayyana hadin Kanunfari da zuma a matsayin na gaba-gaba wajan magance matsalar sanyi da mura.
A yayin da mutum ke fama da kaikayin makogoro, shima wannan hadi na da tasirin da zai magance wannan matsalar.
Yanda ake hadin shine:
Za'a samu Kanunfari kamar kwaya 6 a dan dorasu a wuta a dan gasa.
Sannan a daka su su zama gari.
Sai a zuba babban cokali na zuma a ciki.
Ana shan wannan hadi sau biyu zuwa uku a kullun dan maganin tari mura da kaikayin makogoro.