Farashin litar mai a Najeriya zai sake haura naira dubu daya
Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya wato IPMAN, ta ce farashin litar man fetur a gidajen mai zai zarta naira dubu daya nan da kwanaki masu zuwa.
IPMAN ta ce karin ya zama dole sakamako karin farashin da hukumar fiton man fetur da sanya ido kan sayar dashi ta NMDPRA ta yi.
Alhaji Salisu Ten Ten, shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Arewacin Najeriya wato IPMAN, ya shaida wa BBC cewa, a shekarun baya man fetur daga kasashen waje ake shigo dashi, sai gashi kuma bayan matatar man fetur ta Dangote ta fara aiki sai aka daina shigo da man.
Ya ce, " A lokacin da ake shigo da mai daga kasashen waje akwai harajin naira 10 kan kowacce lita da duk wanda ya shigo da mai yake biyan hukumar NMDPRA, to a yanzu saboda an daina shigo da man sakamakon matatar mai ta Dangote sai dillan man suk...







