Kyan fuska na daya daga cikin abubuwan da Mata ke nema ruwa a jallo sukan kashe makudan kudade wajan gyaran fuskarsu.
Ko da yake a yanzu har maza ma na yin gyaran fuskar saboda zamani.
Ga bayanai dalla-dalla kan yanda za'a yi gyaran fuska da kayan gargajiya na gida.
Maganin Kyan fuska da dankali
Ana cin dankalin Hausa ko a shafashi a fuska dan kyan fuskar da kawar da duk wani datti da duhun fuskar.
Yana kuma maganin takurewar fuska irin na tsufa.
Dan samun wannan armashi, a ci dankalin Hausa ko a rika shafashi a fuskar akai-akai.
Maganin Kyan fuska da Tumatir
Tumatir na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajana gyaran fuska.
Yana maganin tattarewar fuska, idan fuska na yawan yin maiko, Tumatir na maganin hakan, yana kawar da duhun fuska wanda hasken ran...