Friday, July 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Wata Sabuwa: An baiwa Ali Nuhu Wa’adi ya fito ya tallata Shugaba Tinubu ko a kwace mukamin da aka bashi

Wata Sabuwa: An baiwa Ali Nuhu Wa’adi ya fito ya tallata Shugaba Tinubu ko a kwace mukamin da aka bashi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa an baiwa Ali Nuhu Wa'adin sati daya ya fito ya tallata Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ko a kwace mukamin da aka bashi. Daya daga cikin jaruman masana'antar Kannywood ce ta fallasa hakan. Tace ana zargin Rarara ne ya kai gulmarsa sama cewa baya shiga harkar yiwa shugaba Tinubu yakin neman zabe da yake yi, shiyasa aka saka masa wannan wa'adi. https://www.tiktok.com/@yahayyayusoop2/video/7659455781049486612?_r=1&_t=ZS-97pJYeuBWYn
Kalli Bidiyon: Masu cewa ina Tiktok ba Dankwali haka na ga damar yi>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Aina’u Ade

Kalli Bidiyon: Masu cewa ina Tiktok ba Dankwali haka na ga damar yi>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Aina’u Ade

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Aina'u Ade ta bayyana cewa, ganin damartane ta yi fim da dankwali ko akasin hakan. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa a shafinta inda tace masu zarginta saboda yin Tiktok ba Dankwali haka ta ga damar yi. Aina'u tace zata yi abinda ta ga dama. https://www.tiktok.com/@ainau.adee/video/7659218896284585237?_r=1&_t=ZS-97pISAQkIej
Kalli Bidiyon: Yanda Wata Uwargida ta watsawa Mijinta Manja a fararen kayansa bayan da ya je gaisheta da abokansa bayan ya mata kishiya

Kalli Bidiyon: Yanda Wata Uwargida ta watsawa Mijinta Manja a fararen kayansa bayan da ya je gaisheta da abokansa bayan ya mata kishiya

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wata uwargida ta watsawa Mijinta Man ja bayan da yayi aure ya je gaisheta shida abokansa. Bidiyon lamarin ya dauki hankula a kafafen sadarwa inda wasu ke yaba mata, wasu sun ce bata kyautawa kanta ba. https://www.tiktok.com/@aliyushehu021/video/7659154373397990676?_r=1&_t=ZS-97nshTDGbKr
Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta Gwamnati a yau, Litinin 6 ga watan Yuli na shekarar 2026 ya kamane akan Naira ₦1,370.33 akan kowace dala. A kasuwar bayan fage ta garuruwan Kano, Abuja, Lagos da Fatakwal kuwa farashin dalar ya kamane akan Naira 1,385 zuwa Naira ₦1,400 ya danganta idan mutum saye ko sayarwa zai yi.