Hotuna: Kasar Libya ta kulle ‘yan kwallon Najeriya a filin jirgi ta hanasu zuwa ko ina
Kungiyar 'yan Kwallon Najeriya ta Super Eagle tana can a filin jirgin kasar Libya a tsare inda aka hanasu zuwa ko ina.
'Yan kwallon dai sun je kasar ta Libya ne dan buga wasa zagaye na biyu da kungiyar kwallon kafar kasar ta Libya bayan sun yi nasara da sakamakon 1-0 a zagayen farko da aka buga a Najeriya.
Awanni kadan kamin saukar jirgin na 'yan Super Eagle a Libya sai aka canja masa wajan sauka zuwa wani birni me nisa tsakaninshi da inda za'a buga wasa.
Bayan saukar 'yan kwallon Najeriyar sai ba'a basu motar da zata kaisu inda zasu buga wasan ba, sannan rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta yi kokarin samarwa da 'yan wasan Najeriyar motar da zata kaisu filin wasan amma hukumomin kasar ta Libya suka hanasu fita daga filin wasan.
Ana ganin wannan kamar ramuwa kas...








