‘Matatar mu tana iya samar da man fetur fiye da abin da ake bukata a Najeriya’
Shugaban gamayyar kamfanonin Dangote wanda ke da matatar mai ta Dangote Refinery ya ce matatar ta shiya tsaf domin fara sayar da tataccen man fétur da disel har ma da kanazir ga gidajen man kasar.
Alhaji Aliko Dangote ya shaidawa BBC matatar tana iya samar da fiye da man da ake bukata a kasar.
''Inda mu ke ciki yanzu mun soma yin mai, muna jiran su zo su soma karba saboda abinda aka yi a sabon tsari shi ne za su ba mu man fetur da za mu sarafa wanda za mu basu'', in ji shi.
Ya kara da cewa kamfanin mai na kasa NNPCL ne ke da alhakin saka farashin litar man da matatar tasa za ta fitar:
''Wajan saka kudin mai ba a hannunmu yakeba, a hanun NNPC yake ,kawai abinda zan iya tabbatar cewa a yanzu muna da man fetur da Kananzir da disel, duk wadannan wadanda za mu iya ba wa Najeriya fiy...








