Da Duminsa: Bayan Rikicin Wike da Sojan Ruwa, shugaba Tinubu yace Sojoji sun cancanchi yabo
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa kokarin sojojin Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu da sauran 'yan Najeriya su samu tsaro.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron kungiyar Mawallafa jaridu ta kasa
Yace lallai Najeriya na fuskantar Kalubalen tsaro.
Sannan ya jadada goyon bayan sojojin da ke sadaukar da rayuwarsu dan samar da tsaron.








