Ji Ainahin dalilin da yasa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa
Rahotanni sun bayyana cewa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wucin gadi inda yace zai taci hutun sai abinda hali yayi.
Ya bayyana dalilin cewa, wani daga cikin iyalansa ne ba lafiya shiyasa ya dauki wannan mataki duk da yake bai masa dadi ba.
Saidai a binciken da jaridar Daily Nigerian ta gudanar, ta gano cewa ba haka abin yake ba.
Jaridar tace wasu na kusa da shugaban kasa ne suka fara sakawa Ajuri ido kan cewa mukaman da yake rike dasu sun masa yawa kuma sun ci karo da aikinsa na matsayin me magana da yawun shugaban kasa.
Dan hakane suka bukaci ya zabi daya daga cikin mukaman da yake rike dasu ya ajiye sauran, jaridar tace na hannun damar shugaban kasar, sun dauka cewa zai ajiye aikin magana da yawun shugaban kasa ne amma sai ya zabi ya ci ga...





