An Nad’a Matashi Dan Shekara 25 Sarki A Jihar Jigawa
Mai Martaba Sarkin Ringim Alhaji Dr Sayyadi Muhammad Con Ya Nada Matashi Dan Shekara 25 Matsayin Sarkin Karamar Hukumar Taura, Hakan Ya Biyo Bayan Rasuwar Mahaifinsa Marigayi Rabiu Ali Sa'ad Wanda Shi ma Ya Gaji Mahaifinsa.
Al'ummar Karamar Hukumar Taura Sun Yi Dafifi Da Murnar Kasancewar Wannan Matashi Akan Gadon Mahaifin Nasa.
Muna Addu'ar Allah Ya Kama Masa, Ya Jikan Sarkin Taura.
Daga Mall Ahmad Ringim