Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yadda ake amfani da tsinken gwajin ciki

Gwajin Ciki
Tsinken Gwajin ciki na bayar da sakamako me kyau idan aka yi amfani dashi yanda ya kamata. Saidai kamin a yi amfani dashi, masana sun ce ya kamata a bari sai bayan kwnaki 10 banyan yin jima'i, ko kuma idan ana son sakamako wanda yafi kyau a bari sai bayan kwanaki 14, wasu ma sun ce kamata yayi a bari sai bayan kwanaki 21 da yin jima'i yayin da wasu suka ce a bari sai idan ba'a ga jinin al'ada ba. Shawara anan itace, idan kin kagara ki ga sakamakon kina iya yin gwajin a duka lokutan guda 3 ko hudu, watau ki yi bayan kwanaki 10 da bayan kwanaki 14 da bayan kwanaki 21 da kuma bayan baki ga jinin al'ada ba. Yanda ake amfani da tsinken gwajin ciki shine, Ana samin kofi ko mazubi sai a yi fitsari a ciki, sai a saka rabin tsinken a cikin fitsarin. Sai ki fiddoshi ki ajiyeshi a kwance ...

Yadda ake gwajin ciki da fitsari

Gwajin Ciki
Gwajin ciki da fitsari shine mafi bada sakamako me kyau. Idan dai an yi gwajin bayan kwanaki 10 zuwa 14 da yin jima'i to lallai za'a ga sakamako me kyau sosai. Akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan gwajin ciki da fitsari amma wanda suka fi shahara kuma likitoci suka fi yadda dashi shine na tsinken gwajin ciki da ake sayarwa a kyamis. Ana samun mazubi ne ko kofi sai a yi fitsarin a ciki si a saka Rabin tsinken gwajin cikin a ciki, sai ki yi kamar kina kirge da yatsunki, ki kirga 7 ko 10, shikenan sai a cire, a ajiye shi a kwance. Yawanci za'a iya ganin sakamakon gwajin cikin minti 1 ko zuwa 5. Idan tsinken ya nuna layi biyu to kina da ciki amma idan ya nuna layi daya, baki da ciki. Masana sunce zai fi kyau a bari sai an yi batan wata kamin a yi duk wani gwajin dau...
Bayan haihuwar ‘ya’ya 2, Tauraron mawakin Najeriya, Davido da budurwarsa, Chioma zasu je a daura musu aure a Legas

Bayan haihuwar ‘ya’ya 2, Tauraron mawakin Najeriya, Davido da budurwarsa, Chioma zasu je a daura musu aure a Legas

Nishadi
Bayan kwashe shekaru suna soyayya hadda samun 'ya'ya 2, karshe Tauraron mawakin Najeriya, Davido da budurwarsa Chioma zasu je a daura musu aure a Legas. Zadai a musu daurin auren gargajiyane da ake cewa Traditional Wedding. Kuma za'a daura aurenne ranar 25 ga watan Yuni, kamar yanda wasu majiyoyi auka ruwaito. Shima dai Davido da kansa ya tabbatar da hakan.
Fasarar Jawabim Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Mulkin Dimokradiyya

Fasarar Jawabim Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Mulkin Dimokradiyya

labaran tinubu ayau, Siyasa
RANAR DEMOKARADIYA.12/JUNE/2024. Ya ku yan uwanayan Najeriya bari mu fara da taya juna murnar sake ganin zagayowar ranar Demokaradiya a yau, ranar sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Wannan ranar ta zo dai dai da cikar kasar mu shekaru Ashirin da biyar a cikin mulkin Demokaradiya ba tare da katsewa ba. A rana irin ta yau, shekaru talatin da daya baya, muka kaddamar da kudirin mu na zamowa al`ummar da ta yi cikakkiyar amincewa da Demokaradiya. Ba abu ne mai sauki ba, kusan ma cike yake da hadarin gaske ta inda cikin shekaru shida da suka biyo baya sai da duk muka rikide muka zamoyan gwagwarmayar kwatan yancin kanmu a matsayin mu nayan kasa kuma halittun Allah a ban kasa. A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa ha...

Gwajin ciki da sugar

Gwajin Ciki
Gwajin ciki da Sugar ana yinshine ta hanyoyi kamar haka: Ana samun kofi ko kwano ko kuma mazubi a yi fitsari a ciki. Bayan nan sai a zuba sukari a ciki. Yanda ake gane idan ciki ya shiga: Idan mace na da ciki, bayan ta hada fitsarin ta da sukari, zata ga ya yi kulalai. Yanda ake gane babu ciki: Idan mace ta bata dauki ciki ba, bayan ta hada sukarin da fisarin zata ga suka yin bayi kula lai ba. Menene ingancin gwajin ciki da sugar? Gwajin ciki da sugar hanyace ta gargajiya wadda ake amfani da ita wajan gano mace na da ciki ko bata dashi. Saidai babu wani binciken masana lafiya daya tabbatar da cewa wannan hanya na aiki wajan gane mace na da ciki ko bata dashi.
Nasan cewa matakan dana dauka a mulkina sun saka mutane wahala>>Shugaba Tinubu

Nasan cewa matakan dana dauka a mulkina sun saka mutane wahala>>Shugaba Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan matakan da gwanatinsa ta dauka na tayar da komadar tattalin arziki sun kawo wahala. Ya bayyana hakane a jawabin da yayi da safiyar yau na ranar Dimokradiyya. Inda yace yana sane da wahalar da 'yan kasa suke sha. Ya bayyana cewa amma daukar matakan dolene dan dora Najeriya a turba me kyau wadda zata daina dogaro akan man fetur kadai dan samun kudin shiga. Ya bayyana cewa wannan abu ne da ya kamata a yi shi da dadewa amma shuwagabannin da suka gabata ba su yi ba.

Gwajin ciki na sati daya

Gwajin Ciki
Bayan yin jima'i ba tare da kariya ba ta kwaroron roba, watau Kondom, mace zata iya daukar ciki. Kuma zaki so yin gwaji da ganin kin dauki cikin ko baki dauka ba? Saidai masana sun bayyana cewa, sati daya yayi kadan ki gane cewa kin dauki ciki ko baki dauka ba. Mafi abinda ya dace a yi shine a dakata har sai bayan kwanaki 10 zuwa sati 2 da yin jima'i kamin a fara yin gwajin ciki. Wasu kuma sun bayar da shawarar a jira sai bayan daukewar jinin al'ada. Ana iya yin gwajin ciki ranar farko da aka yi batan wata. Jira zuwa lokaci me tsawo watau sati 3 zuwa 4 bayan an yi jima'i ba tare da kariyar kwaroron roba ba, watau kondon kamin a yi gwajin ciki, ya fi bayar da sakamako me kyau.

Tauraruwar Fina-Finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da shuwagabannin kasashen Duniya saboda kyalewa da suka yi anawa Falas-dinawa kisan kiyashi

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Tauraruwar Fina-finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da kisan da akewa Falasdinawa. Sannan kuma tace Tana zargin shuwagabannin kasashen Duniya da suka saka Ido suna ganin yanda akewa Falasdinawa kisan kiyashi. Jolie dai dama ta kasance me son tallafawa mutane inda a baya ta yi aiki da majalisar dinkin Duniya wajan bada ayyukan agaji.
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da tayin yin Sulhu da kasar Israela. Shugaban Hezbollah din, Hassan Nasrallah ne ya bayyana haka. Fada na ci gaba da kazancewa tsakanin kasar Israela da Hezbollah. Ko da a jiya sai da Hezbollah tawa kasar Israela ruwan bamabamai masu yawa. Kungiyar dai ta Hezbollah ta bayyana cewa tana goyon bayan samun 'yancin Falasdinawa.
Tinubu ya ce a kamo maharan da suka kashe mutum 50 a Katsina

Tinubu ya ce a kamo maharan da suka kashe mutum 50 a Katsina

Siyasa
Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su. Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar a ranar 11 ga watan Yuni, 2024 yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-hare a ƙasar. A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-hare, shugaban ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma taarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya da sauran masu tayar da zaune tsaye da kuma baƙin ciki a kowane ɓangare na ƙasar. Shugaban ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’...