Yadda ake raka atanil fajr
FALALAR RAK'ATAYIL FAJR
Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.Malamai sun ce ana karanta Fatiha ne da Qul Ya ayyuhal Kafirun, da kuma fatiha da Qul Huwal-Lahu acikinta. KUMA ana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIF...