Allah Sarki: Ji yanda auren wata mata ya mutu saboda kissar kishiya
Wata baiwa Allah da labarinta ke cike da ban tausai ta bayyana yanda aurenta ya mutu saboda kissar Kishiya.
Ta bayyana hakane a zauren yanar gizo na Arewa up.
Ga dai yanda labarin yake kamar yanda ta badashi:
Ta fara shimfida kamar haka:
"yadda aure na ya mutu
assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh yadda aure na na biyu ya mutu a silar kissar kishiya a gaskiya maza idan kunsan Baku Isa da matanku na gida ba kudaina yinkurin Kara aure sbd ku kanku Baku Isa kuce ba bare Kuma mu da aka aura"
Ta ci gaba da bayar da labarin kamar haka:
"wallahi na fada Miki bansan me ya faru ba Kinga an kaini gidansa ranar Friday to Kuma Daman gaskiya kamar Yana tsoron matar tasa to kwana na uku muka fara rabon kwana to yaje yayi mata kwana 2 ya dawo yayimun kwana 2 ya koma gidanta to wa...