Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci.
Shahararriyar Manhajar haƙo sulalla ta Tapswap ta hanyar TON Blockchain ta ce ta jinkirta ranar bajakolin kasafin sulalla ga masu amfani da shi zuwa wani lokaci da ba su sanar ba, yayin da ma'aikantan su ke kokarin neman karin hanyoyin da za su inganta shi domin amfanar mutane da yawa.
Shugaban sashen sadarwa na Tapswap John Robbin ne ya bayyana hakan a dandalin sadarwarsa na X ranar Laraba.
Dandalin wanda ke buƙatar masu amfani da shi da su rika danna alamar da ke tsakiyar manhajar Tapswap a Telegram don hakar sulalla a kwanan nan ya samu karbuwa a tsakanin 'yan Najeriya inda suke duƙufa wajen latsa fuskar wayarsu don neman kudi, kuma ya tara mutane sama da Miliyan 50 tun bayan da aka kaddamar da shi a ranar 15 g...