DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu.
Abin jira dai a gani shine ko ‘yansandan zasu bi umarnin Kotun, ganin cewa a baya ma an samu wata kotu ta bayar da umarnin hana sauke Aminu Ado Bayero amma umarnin bai yi amfani ba?
Rigimar sarautar Kano dai ta dauki hankula sosai a kasarnan inda a karon farko aka samu sarakuna biyu a jihar da kowane ke cewa shine sarkin Kano.
Shugaban karamar Hukumar Munya ta jihar Naija, Malan Aminu Najume ya koka kan ayyukan ‘yan Bindiga a karamar hukumar tasa inda ya nemi a kubutar da mutanensa daga hannun ‘yan Bindiga.
Ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace ‘yan Bindigar sun shiga garin kuci inda suka kashe mutane 7 da kuma sace 150.
Ya bayyana cewa, cikin wadanda aka kashe akwai jami’an tsaro 4 da kuma ‘yan Bijilante da wasu mutanen garin.
Saidai ya jinjinawa jami’an tsaron dake garin inda yace aun kashe guda 25 daga cikin ‘yan Bindigar.
Yace yawanci ‘yan Bindigar na zuwa ne daga jihar Kaduna inda suke musu aika-aika daga bisani su koma Kadunar.
Yace sun shiga garin da mashina kusan 100 kuma sun rika bi gida-gida suna daukar wanda suke son yin garkuwa dasu da suka hada da mata.
WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu.
Shi dai Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya zargi Nuhu Ribadu ne da baiwa tsigaggen sarkin Kano Aminu Ado Bayero jirgi biyu tare da jami’ań tsáro dan su banƙara a shígar da da shi masarautar Káno.
Ya ce kuma Ganduje ne ya je wajań mai bawa shugaban kásar shawara kan harkar tsáro wato Nuhu Ribadu dómin aikata wannań mummunan aiki.
A céwar mataimakin Gwamnan duk abinda za muyi zamuyi dan mu tabbatar haka bata faru ba, muna gidan Sarki dukkanin mu jami'an Gwamnati.
Me zaku ce?
Lafiya ƙalau mu ka yi zaɓen farko a Kano a 2019, amma su ka ƙirƙiri fitinar ‘inconclusive’, suka kawo ‘yan ďàbà suka raunana mutane suka kwace zaɓen.
Lafiya ƙalau majalisa ta yi dokar cire sarakuna babu tarzoma, kowa ya koma sha’aninsa, amma daga baya su ka kawo sojoji da 'yan ďaba suna tada husuma a gari.
Allah Ka yi mana maganin duk wanda ke da hannu a haɗa wannan fitina.
Rahotanni sun nuna yanda Israela ta kai wani mummunan hari a wajan sansanin 'yan gudun Hijira dake Rafah.
Harin yayi sanadiyyar wuta ta tashi a sansanin inda mutane akalla 50 suka kone kurmus.
An ta ganin gawarwakin mutane sun kone ana zakulosu a bidiyon da suke ta yawo a shafukan sada zumunta.
Saidai hakan na zuwane bayan da kotun majalisar dinkin Duniya ta baiwa Israelan umarnin daina kai hari Rafah:
https://twitter.com/CensoredMen/status/1794815544425873773?t=YnxpkOAzQnE8MDsF5KvKOg&s=19
https://twitter.com/syylllia/status/1794855529753506121?t=vZml1Ho1zA4AK7Yvdj7yew&s=19
https://twitter.com/jacksonhinklle/status/1794824350195167660?t=5qymwlqoX0GFP57gJcujrQ&s=19
Abin jira a gani shine wane mataki majalisar dinkin Duniyar zata dauka tunda dai gashi I...
Wasu 'yan Najeriya 6 sun gamu da ajalinsu bayan da aka kashesu a kasar Afrika ta kudu.
Saidai da bidiyon faruwar lamarin ya bayyana a kafafen sada zumunta, 'yan kasar Afrika ta kudun sun rika yabawa wanda suka kashe 'yan Najeriyar.
Sun yi fatan a kara kashe 'yan Najeriyar da yawa.
Sojojin Najeriya sun kai samame maboyar 'yan ta'adda a Jihar Kaduna inda suka kashe guda 6.
Sojojin sun yiwa 'yan Bindigar kwatan baunane inda suka kashesu tare da kwace makamai da yawa a hannunsu.
Lamarin ya farune bayan da sojojin suka samu bayanai akan ayyukan 'yan Bindigar a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari ranar Friday, May 24, 2024.
Sojojin sun je hanyar da 'yan Bindigar zasu wuce inda suka musu kwantan bauna, suna zuwa kuwa suka afka musu.
An yi bata kashi sosai inda daga baya 'yan Bindigar suka tsere:
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa 'yan Najeriya cikin wahala.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu.
Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 wanda 2 dolene amma ba'a daukesu yanda ya kamata ba.
Yace Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin cire tallafin man fetur da kuma na dala.
sannan sai kuma shiga lamarin juyin mulkin kasar Nijar.
Yace gyaran tattalin arziki ba'a yinshi dare daya. Yace dolene sai an dage, yace idan aka dauki matakan da suka dace, cikin shekaru 2 Najeriya zata iya daukar saiti.
Ya bayar da misalin yanda kamfanin Total Energy suka zagaye Najeriya suka je kasar Angola suka zuba jarin dala biliyan 6.
Obasanjo yace maganar gaskiya dole a f...