Sunday, April 26
Shadow

Duk Labarai

Kai Duniya: Ji abinda wata matashiya daga Arewa ta yi bayan data yi cikin Shyègyè ta haihu da ya dauki Hankula

Kai Duniya: Ji abinda wata matashiya daga Arewa ta yi bayan data yi cikin Shyègyè ta haihu da ya dauki Hankula

Duk Labarai
Wata matashiya daga Arewa da ta yi cikin shege ta haihu ta kuma mayar da dan inda ya fito ta dauki hankula. Ta aikawa Malam tambaya ne inda tace ta tuba kuma tana neman yanda Allah zai yafe mata. Abin dai ya baiwa mutane mamaki amma Malam yace idan da gaske ta tuba Allah zai yafe mata idan ta maye abinda ta aikata da kyakkyawa. https://www.tiktok.com/@mhaliru92/video/7592682873547787541?_t=ZS-92tcnLlGekz&_r=1
Wata Sabuwa: Bayan da aka bukaci ya je ICPC ya bayar da hujja kan zargin da yakewq shugaban Hukumar NMDPRA, Dangote yace ya janye zargi da yake

Wata Sabuwa: Bayan da aka bukaci ya je ICPC ya bayar da hujja kan zargin da yakewq shugaban Hukumar NMDPRA, Dangote yace ya janye zargi da yake

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangote ya janye zargin da yakewa shugaban Hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmad a gaban Hukumar ICPC. Dangoten ya janye zargin da yake wa Ahmad ne inda yace ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa 'ya'yansa kudin makaranta a kasar Switzerland. Wata Majiya tace Dangoten ya janye zarginne bayan da aka bukaci ya je da kansa ba aiken Lauya ba ya gabatar da hujjoji a gaban ICPC kan wannan zargin da yake. Hakanan Wata Hujja da aka samu game da janye wannan korafi da Dangoten yayi shine EFCC ta fara bincike kan lamarin. Saidai ICPC tace duk da wannan Janyewar da Dangote yayi ba zata yi watsi da binciken da takewa Ahmad ba, tace ta ma aika da bukatar bincike makarantar da ake zargin Ahmad din ya kai 'ya'yansa. Ahmad dai tun tuni ya sauka daga kan mukaminsa ...
Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban Buhari ya yi ta neman Masu gaskiya irinsa da zai baiwa Mukami amma ya kasa samun ko da mutum daya>>Inji Hadimin Shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad

Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban Buhari ya yi ta neman Masu gaskiya irinsa da zai baiwa Mukami amma ya kasa samun ko da mutum daya>>Inji Hadimin Shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nemi wadanda zai baiwa mukaman Siyasa masu gaskiya da kishin Najeriya irinsa amma ya kasa samu. Hadiminsa, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da Ali Jita yayi dashi. Yace Buhari ya gaya musu cewa a tsawon lokacin da ya dauka yana kokarin neman Mulki, ya manta bai nemi mutane nagartattu ba da zai yi aiki dasu. Yace sai bayan da ya ci zabe, ya je gida ya kwanta amma Bacci ya ki zuwa, yace sai ya tuna wata ma'aikata da ke da matsala, sai yayi tunanin wanene zai dakko me irin ra'ayinsa ya baiwa wannan ma'aikata amma sai ya kasa samun ko da mutum daya. Yace a wannan lokacinne yasan cewa bai samarwa kansa abokan aiki ba. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7592575748817440008?_t=ZS-92tY3O7k8DA&_r=1
A shekarar 1983 manyan sojoji sun sameni suka ce zasu yiwa Tsohon Shugaban kasa, Shehu Shagari Juyin mulki dan in zama shugaban kasa amma nace bana so>>Inji Obasanjo

A shekarar 1983 manyan sojoji sun sameni suka ce zasu yiwa Tsohon Shugaban kasa, Shehu Shagari Juyin mulki dan in zama shugaban kasa amma nace bana so>>Inji Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a shekarar 1983, manyan sojoji sun sameshi suka ce zasu yiwa shugaban kasa a wancan lokacin, Shehu Shagari Juyin Mulki dan shi Obasanjon ya zama shugaban kasa. Saidai Obasanjon yace musu baya so. Yace dalilinsa shine su suka Kafa Dimokradiyya diyya a Najeriya dan haka ba zai zama cikin wanda zasu rusata ba. Hakanan shima tsohon shugaban kasar Soji, Janar Ibrahim Badamasi ya tabbatar da wannan labari na Obasanjo.
Da Duminsa: Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana Muguntar da DSS suka shirya mai da zarar an bayar da Belinsa

Da Duminsa: Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana Muguntar da DSS suka shirya mai da zarar an bayar da Belinsa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar 'yansandan Farin kaya ta DSS na shirin sake kama tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami da zarar an bayar da belinsa. Malami ne ya bayyana hakan ta bakin me magana da yawunsa, Muhammed Bello Doka. Yace DSS na shirin yi masa wannan abu da ya kira take hakinsa ne bayan da kotu ta bayar da belinsa. Malami yayi zargin cewa, DSS sun dana tarko akansa suna jiran a bayar da belinsa su sake chafkeshi.
Da Duminsa:Wata Majiya ta bayyana ainahin Abinda Kwankwaso yaso yiwa Abba wanda shine ya baiwa Abban Haushi yasa yake son komawa APC

Da Duminsa:Wata Majiya ta bayyana ainahin Abinda Kwankwaso yaso yiwa Abba wanda shine ya baiwa Abban Haushi yasa yake son komawa APC

Duk Labarai
Wata majiya daga Kano tace ainahin abinda ya kawo rashin jituwar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da shugaban Tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso shine. Kwankwason ya so saka 'yan majalisar jihar Kano su tsige Abba. Wannan banai na ta yawo ne a kafafen sada zumunta inda a wata majiyar kuma aka rika ruwaito cewa, Kwankwaso baya son Abba ya sake tsayawa takarar Gwamnan Kano ne a shekarar 2027 inda yake son kawo wani dan takara na daban. https://twitter.com/i/status/2008888990062223473 https://twitter.com/i/status/2008973814240055306