Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan yaki ya barke a Kano to shugaban kasa, Tinubu ne sila.
Atiku ya bayyana cewa dalili kuwa shine Tinubu ya aika sojoji su je Kano su nada Sarki.
Bayan da majalisar jihar Kano ta rushe duka sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje ya kirkiro, an mayar da tsohon sarki, Muhammad Sanusi akan kujerar sarautar Kano inda aka tsige Aminu Ado Bayero.
Saidai Aminu Ado Bayero bisa rakiyar sojoji wadanda ake kyautata zaton Gwamnatin tarayya ce ta bashi su ya koma Kano inda ya yada zango a karamar fadar sarki dake Nasara.
Shi kuma sabon sarki, Muhammad Sanusi II yana can fada yana karbar mubaya'a daga hakimai da sauran mutanen gari.
An dai zargi me baiwa shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu da hannu a...