Jaruman Kannywood da suka rasu a 2024
Har yanzu masana'antar Kannywood da masu bibiyarta suna tunawa tare da jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi El'mu'az Birniwa, wanda ya rasu a daren Laraba, 4 ga Disamban 2024 a Kaduna.
Irin yanayin da mawaƙin ya yi rasuwar fuju'a ce ta sa jimaminsa da ake yi ya ɗauki lokaci, kamar yadda ake yi idan an yi mutuwar farat-ɗaya.
Mawaƙi El-Mu'aza ya shiga sahun irin su Saratu Daso da Mustapha Waye da darakta Aminu S. Bono wajen yin irin rasuwar ta fuju'a.
A daidai wannan lokaci da muka yi ban-kwana da shekarar 2024, BBC ta tattaro wasu ƴan masana'antar da suka bar duniya a shekarar.
Fatima Sa’id (Bintu)
A ranar Lahadi 11 ga Fabrairun 2024 ne Allah ya yi wa jaruma Fatima Sa'id, wadda aka fi sani da Bintu Dadin Kowa rasuwa.
Jarumar wadda ta fi yin fice a shirin na tashar Arewa24 t...