Saturday, June 27
Shadow

Duk Labarai

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta gwamnati a yau, Alhamis 18 ga watan Yuni na shekarar 2026 ya kamane akan Naira ₦1,360 akan kowace dala. A kasuwar bayan fage kuwa, Farashin dalar ya kamane akan Naira 1,400 akan kowace dala. 'Yan kasuwar bayan fagen na sayen dalar akan Naira ₦1,392 zuwa Naira ₦1,395 a yayin da suke sayarwa akan Naira ₦1,400 zuwa Naira ₦1,402.
Likitoci 550,000 ne suka rage a Najeriya, gida 16,000 sun tsere zuwa kasashen Turawa

Likitoci 550,000 ne suka rage a Najeriya, gida 16,000 sun tsere zuwa kasashen Turawa

Duk Labarai
Wata kungiyar Likitocin Najeriya ta koka da yawan tserewar Likitoci daga Najeriya zuwa kasashen Turawa. Kungiyar tace a yanzu Likitoci 55,000 ne suka rage a Najeriya. Wanda sune ke kula da 'yan Najeriya mutane Miliyan 220. Likitocin sun bayyana hakane a wata ganawa da suka yi a Asibitin masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa dake Yaba Lagos. Shugaban kungiyar Likitocin, Prof Omoti Ernest ya bayyana cewa, sun yiwa Likitoci 130,000 Rijista amma zuwa yanzu guda 55,000 ne kadai ke aiki a Najeriya. Hakan na nufin duk likita daya yana duba marasa lafiya tsakanin 3,600 zuwa 4000. Sun yi kiran a dauki matakin hana likitoci tserewa daga Najeriya dan gujewa tabarbarewar harkar Lafiya a kasar.
Kalli Bidiyon sabbin gidajen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ginawa Alkalai saidai da yawa na zargin cewa toshiyar baki ce

Kalli Bidiyon sabbin gidajen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ginawa Alkalai saidai da yawa na zargin cewa toshiyar baki ce

Duk Labarai
An yi bikin kaddamar da gidajen da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike suka ginawa alkalai na kotunan daukaka kara. Saidai hakan ya jawo zarge-zarge a zukatan 'yan kasa. Da yawa na zargin cewa, an gina gidajenne a matsayin toshiyar baki ga alkalan. https://twitter.com/i/status/2067486725107040544
Bayan da cacar baki ta yi yawa tsakanin Rarara da Davido: An bayyana kudin da kowannensu ya mallaka

Bayan da cacar baki ta yi yawa tsakanin Rarara da Davido: An bayyana kudin da kowannensu ya mallaka

Duk Labarai
A yayin da cacar baki ta yi yawa tsakanin Rarara da Davido, masoyansu sun fitar da bayanan abubuwan da kowanne ya mallaka. An bayyana yawan kudin da kowannensu ya mallaka. Da yawan mabiyan da kowanne su ke da a kafafen sada zumunta. Da yawan motocin da suka mallaka. Da yawan gidajen da suka mallaka. Da dai Sauransu, saidai duka wannan hasashene musamman ma maganar kudi.
A karin farko, ‘yan majalisar wakilai sun murza gashin baki inda suka cewa, shugaba Tinubu ko dai ya dakatar da duk wani shirin siyasa da yakin neman zabe ya magance matsalar tsaro, ko kuma ya sauka kawai

'Yan majalisar wakilai marasa rinjaye sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dakatar da maganar yakin neman zabensa a 2027 ya mayar da hankali wajan magance matsalar tsaro. Sun bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda suka ce matsalar tsaro ta kai makura a kasarnan inda suka kawo misali da abinda ya faru da janar Rabe Abubakar a jihar Katsina. 'Yan majalisar sun zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da nuna halin ko in kula game da matsalar tsaron inda yafi mayar da hankali wajan yakin neman zabensa.
Gwamnatin tarayya ta bude sabbin tashoshin talabijin 100 da ‘yan Najeriya zasu rika kallo Kyauta

Gwamnatin tarayya ta bude sabbin tashoshin talabijin 100 da ‘yan Najeriya zasu rika kallo Kyauta

Duk Labarai
Gwammatin tarayya na sanar da bude gidajen talabijin 100 da 'yan kasa zasu rika kallo kyauta ba tare da biyan kudi duk wata ba. A jumlace an musu sunan FreeTV. Fadar shugabab kasa ce ta sanar da wannan a ranar Laraba. Sanarwar tace gidajen Talabijin din sun hada dana labarai dana wakoki dana wasannin yara dana ilimi a ciki da wajen Najeriya. Sanarwar tace wannan mataki ne na inganta kafofin watsa labarai zuwa na zamani.
Idan Zarmalulun ka na mikewa amma baka ganin Jijiyoyi akwai matsala>>Inji Malama Kausar inda ta bayar da maganin da zaia iya hadawa da kanka a gida

Idan Zarmalulun ka na mikewa amma baka ganin Jijiyoyi akwai matsala>>Inji Malama Kausar inda ta bayar da maganin da zaia iya hadawa da kanka a gida

Duk Labarai
Malama Kausar ta bayyana cewa, idan Zarmalulun mutum ya mike amma bai ga jijiyoyi akai ba to akwai matsala. Hakan na nufin jini baya yawo a wajan yanda ya kamata. Ta bayyana cewa akwai maganin da ake yi wanda shine shan kankana da 'ya'yan kankanar. https://twitter.com/i/status/2067381396314771921
Turawa sun ce wai dala Biliyan $38 na mallaka to ko Matatar man fetur dina kadai ta zarta dala Biliyan $40 kuma ina da kamfanoni da sauran kadarori da basu sakasu a lissafi ba>>Inji Dangote

A wata hira da aka yi dashi, Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, bayanin da turawa suke cewa wai kudinsa dala Biliyan $38 ne ba gaskiya bane. Dangote yace ko matatar man fetur dinsa kawai ta fi Dala Biliyan $40. Sannan kuma akwai wasu kadarorinsa da ba'a sakasu a lissafi ba. Dangote da aka tambayeshi gashi yana da kudi amma baya alfahari sai yace tarbiyyar da ya samu daga gidane ba'a koya musu Alfahari ba. https://twitter.com/i/status/2067288672043446613