Bidiyo: Kasa karanta sabon taken Najeriya da ‘yan Kwallon Najeriya suka yi ya jawo cece-kuce
Bidiyon 'yan kwallon Najeriya a filin wasan da suka buga wasa da kasar Africa ta kudu ya jawo cece-kuce.
Bidiyon ya nuna 'yan kwallon na Najeriya sun ki rera sabon taken ko kuma ince sun kasa rerashi.
Saidai za'a iya cewa, har yanzu mutane da yawa basu kai ga iya taken ba.
https://www.youtube.com/watch?v=9IGhoqFJoFM
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya bayyana cewa, canja taken na daya daga cikin muhimman ayyukan da yake son yi a Najeriya.