Friday, January 10
Shadow

Duk Labarai

Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa a kyale mutane su dandana wahalar Rayuwa watakila hakan zai sa su shiga taitayinsu ta yanda zasu rika kalubalantar azzaluman shuwagabanni. Ya bayyana hakanne da yammacin yau, Juma'a, 7 ga watan Yuni yayin da yake karatun littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna. Malam ya kara da cewa, mutane suna da wakilai a majalisar tarayya idan akwai abinda basa so zasu iya gayawa wadannan wakilai cewa shugaban kasa ya canja idan ba haka ba ...
Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin Kasafin kudi

Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin Kasafin kudi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin kasafin kudi. Gwamnatin zata ciwo bashinne a wannan shekarar ta 2024 kuma zata yi hakan ne dan samar da kudin da zata biya tallafin man fetur wanda zai lakume Naira Tiriliyan 5.4. Kafar yada labarai ta Reuters ce ta ruwaito wannan labari. Saidai Gwamnatin tarayya ta ci gaba da nanata cewa ita fa har yanzu bata biyan tallafin man fetur.
Na cika duk Alkawuran dana daukarwa ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

Na cika duk Alkawuran dana daukarwa ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yayin da ya cika shekara daya da fara mulkin Najeriya, ya cika alkawuran da ya daukarwa yan kasar. Tinubu ya bayyana haka ta bakin ministan yada labarai, Muhammad Idris. Ministab yace tun bayan hawansa mulki, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cika alkawuran tada komadar tattalin arziki. Yace ya cire tallafin dala dana nera da sauransu. Ga bayanin sa kamar haka: “Since taking office a year ago, President Tinubu has done what he promised on the economy: he has removed the fuel subsidy, floated the Naira, and instituted a raft of other reforms including changes to the tax code and waivers for foreign investors in critical industries including mining, energy, and infrastructure.”
Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hajjin Bana, Tsaro
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wasu mahajjata a otal din Emerald Hotel dake Ladipo a jihar Legas suna hadiye hodar Iblis da zasu tafi da ita kasa me tsarki. An kamasu ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuni kamin tashin jirgin su zuwa kasa me tsarkin. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wadanda aka kamadin, Usman Kamorudeen na da shekaru 31, sai kuma Olasunkanmi Owolabi me shekaru 46, akwai kuma Fatai Yekini me shekaru 38, sai Ayinla Kemi.me shekaru 34. Yace an kwace dauri 200 na hodar Iblis din daga hannun wadanda ake zargi.
Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Duk Labarai, Jihar Naija, Tsaro
Mutane aun nutse a ruwa yayin da suka shiga jirgin ruwa dan tserewa harin 'yan Bindiga a garin Gurmana dake karamar hukumar Shirori jihar Naija. Yawanci idan maharan suka kai hari, mutane kan tsere zuwa wani tsibiri har sai kura ta lafa kamin su koma gidajensu. Mutanen daai sun tserene ranar Laraba. Saidai ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga kan tsibirin da suka samu mafaka, mutane 4 sun mutu, bayan da jirgin ruwan da suke ciki yayi hadari.
Sace karafan titin jirgin kasa ya haddasa hadarin jirgin kasan dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja

Sace karafan titin jirgin kasa ya haddasa hadarin jirgin kasan dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja

Duk Labarai
Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana cewa an samu hadarin jirgin kasan dalilin satar karafan dake rike titin jirgin. Hakan ya haddasa aka dakatar da jigilar jirgin ranar Alhamis na dan wani lokaci dan cire jirgin da ya samu matsalar. Saidai me magana da yawun hukumar, Yakub Mahmood ya bayyana cewa duk wanda ya riga ya sayi tikitin jirgin, zai iya amfani dashi har nan da zuwa sati biyu masu zuwa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi

Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi

Siyasa
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi. Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana haka ne a wajen taron Majalisar Koli ta (NEC) Yayin marabtar kungiyar Kiristoci ta (CAN) a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja.. Akume ya ce " ba zan iya biyan direbobi na Naira dubu dari ba domin su 4 ne ya zama wani karin nauyi akaina" Ballantana kungiyar kwadago.. A ina muke samun kudaden da kungiyar kwadago ta buƙata ? Inji shi