Wannan hoton na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dauki hankula ana ta magana akansa.
Hadimin tsohon shugaban kasar, Bashir Ahmad ne ya wallafa hoton a shafinsa na sada zumunta.
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, ba zata amince da kari dan kadan, wanda bai kai ya kawo ba akan Naira Dubu 60 ba.
Kungiyar Kwadago ta NLC dai ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan bayar da dama ga gwamnati ta mata kari akan Naira Dubu 60 na mafi karancin Albashi.
Shugaban kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata ganawa da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace su basu nace wai sai an biyasu Naira Dubu dari hudu ba amma dai abinda suke cewa, shine a biyasu albashi me kyau.
Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta ƙasa a Najeriya ta ce an sake kunna babban layin wutar da aka kashe bayan janye yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka yi.Shugaban ƙungiyar National Union of Electricity Employees (NUEE), Adebiyi Adeyeye, ya faɗa wa jaridar Punch cewa sun kunna layin ne bayan janye yajin aikin a safiyar yau."An janye yajin aiki kuma hakan yana nufin layin ya koma aiki yadda ya dace. An kunna shi tuni," in ji Mista Adeyeye.Sai dai har yanzu akasarin ƙasar na cikin duhu duk da wannan iƙirari da shugaban ya yi.Tun a jiya Litinin kamfanin kula da rarraba lantarki a Najeriya TCN ya ce mambobin ƙungiyar ƙwadago ne suka tilasta wa ma'aikatan lantarkin shiga yajin aikin ta hanyar kashe babban layin.
Wasu 'yan mata da suka dauki hankula a kwanannan su biyu kawayen juna sun je wajan wani mutum dan yin lalata.
Saidai tin da suka tafi wajensa ba'a sake ganinsu ba.
Hakan yasa aka yi kiyasin cewa sun bata.
Saidai daga baya an gano mutumin inda aka kamashi.
Amma ana kan hanyar da za'a kaishi ofoshin 'yansanda, sai ya yi kokarin tserewa wannan yasa 'yansandan suka kasheshi.
An gano cewa, mutumin yana da alaka da wata kungiyar Asiri.
Wasu karin bayanai da suka bayyana kan lamarin sun nuna cewa, mutumin ya baiwa 'yan matan Naira Miliyan daya ne dan su je yayi lalata dasu.
Saidai ashe ajali ne yake kiransu.
Labarin wadannan 'yan mata biyu dai sai ci gaba da kara daukar hankaki yake, domin kuwa zuwa yanzu an gano gawarwakinsu a kusa a gidan mutumin da ya gayya...
Likitocin jihar Yobe karkashin kungiyarsu ta (NMA) basu shiga yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC ba a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar na jihar, Dr Abubakar Kawu Mai Mala ne ya bayyana hakan inda yace duk da yake 'yan uwa ne su da NLC amma basa karkashin kungiyar.
Ya kara da cewa, kuma bangaren lafiya a jihar ta Yobe na da matukar muhimmancin da baza'a kulleshi ba gaba daya.
Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a wannan rana.
Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.
Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi.
Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su ...
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.
Jajirtaccen Dan Sanda DCP Abubakar Guri Ya Rasu
Allah Ya Yi Wa Jajirtaccen Dansanda Mukkadashin Kwamishinan Yansanda (Deputy Commissioner Of Police) Abubakar Mohammed Guri Rasuwa, Yau Litinin.
Allah Ya Jikansa Da Rahama!
Rahotannin da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC da TUC sun amince su janye yajin aiki da suke dan ci gaba da tattaunawa da gwamnati.
An samu wannan matsaya ne bayan zaman da wakilan kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya.
Kungiyoyin zasu zauna da membobinsu gobe dan tattauna maganar janye yajin aikin.
Gwamnatin tarayya ta amince a ci gaba da tattaunawa akan mafi karancin Albashi sama da Naira Dubu 60.
An kashe wani mafarauci Sunday Ijiola a Yewa jihar Ogun inda aka yi tsammanin dabbace.
Atanda Agbobiado ne yayi kisan ranar 28 ga watan Mayu.
Mafarauta kusan 15 ne suka fita farautar inda suka raba kawunansu a cikin daji.
Da Atanda ya tabbatar da abinda ya aikata sai ya tsere.
Wanda aka harba din dan kimanin shekaru 43 ya mutu akan hanyar zuwa Asibiti.
Kakakin 'yansandan jihar Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna bincike akai.
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta murik ta bayyana cewa, yajin aikin da ake zai jefa rayuwar musulmai cikin wahala musamman ma ya dake fuskantar babbar Sallah.
Dan haka kungiyar ta yi kira ga kungiyar kwadago data daga yajin aikin nada sai bayan sallah.
Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta hannun babban daraktanta Professor Ishaq Akintola a yau Litinin.
Ya bayyana cewa wannan yajin aiki zai saka musulmai wahalar ababen hawa dan haka suna kiran da a canja lokacin yin yajin aikin.