Monday, November 23
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Duk da DSS sun janye karar da suka shigar akan zargin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, kotu ta ki amincewa ta bayar da belinsa

Kalli Bidiyon: Duk da DSS sun janye karar da suka shigar akan zargin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, kotu ta ki amincewa ta bayar da belinsa

Duk Labarai
A yau ne dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta janye karar data shigar akan malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ta zargeshi da yiwa wayar babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse. Bayan janye karar, Lauyoyin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun roki kotu da cewa, ta taimaka ta rage sharudan bayar da belin malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda sun yi tsauri. Lauyoyin na Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun bayyana cewa, sun yi iya bincikensu basu samo ma'aikacin gwamnati dake mataki na 17 dake da gida a Maitama ba. Lauyoyin sun kara da cewa, dan haka suna neman a sassauta sharudan bayar da belin na Malam Nasiru. Saidai kotun ta yi watsi da wannan bukatar tasu inda DSS suka sake tasa keyar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai suka tafi dashi. https://twitter....
Kalli Bidiyon: Yanda Fitsararren dan Tiktok, Y America ya saiwa wani Gurgu keken Guragu

Kalli Bidiyon: Yanda Fitsararren dan Tiktok, Y America ya saiwa wani Gurgu keken Guragu

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Y America ya saiwa wani Gurgu keken Guragu. Gurgun Ya roki Y America ne a comment dinsa inda shi kuma ya masa alkawarin zai saya masa Keken. Sai gashi ya cika alkawari inda yace ya tambayi keken an ce masa daga dubu 30, 40, 50 ake sayarwa shine yace bari ya sayawa Gurgun. https://www.tiktok.com/@y834097/video/7654200797575630094?_r=1&_t=ZS-97RtevJgPQY
Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Talata

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Talata

Duk Labarai
A farashin dala a kasuwar Chanji ta Gwamnati a yau, Talata, 23 ga watan Yuni 2026, farashin yana akan Naira ₦1,366.41 ne akan kowace dala. A kasuwar bayan fage ta jihohin Kano, Abuja, Lagos da Fatakwal kuwa, Farashin dalar ya kai Naira 1,410, zuwa Naira 1,420, ya danganta idan saye ko sayarwane za'ayi. Rahotanni sun ce bukatar dala daga masu fita zuwa kasashen waje akan kasuwanci ko wasu sha'ani na ci gaba da karuwa.
Kalli Bidiyon: Matar Ahmad XM, Safeera ta masa tonon Silili inda ta bayyana yanda suka rika aikata lalata kamin su yi aure

Kalli Bidiyon: Matar Ahmad XM, Safeera ta masa tonon Silili inda ta bayyana yanda suka rika aikata lalata kamin su yi aure

Duk Labarai
Bayan da Tauraron Tiktok kuma dan Crypto, Ahmad XM ya mayar da tsohuwar matarsa, Safiya. An samu Rahotanni dake cewa, rikici ya kunno kai a cikin gidansa inda matarsa, Safeera ta tayar da balli. A wani sako data wallafa a shafukan sada zumunta an ji tana cewa, baya sonta kuma makaryacine sannan ya cika son kansa. Sannan daga baya an ji wata sautin murya wadda akace ta AhmadXM ce inda yake bayyana cewa Safeera ta kyaleshi ba zai aureta ba. Muryar an dauketa ne tun kamin ya aureta a yayin da ya riga ya auri Safiya. Saurari yanda ta kaya a Bidiyon kasa: https://www.tiktok.com/@northysite/video/7654497787056295188?_r=1&_t=ZS-97Rifa6S1qh
Kalli Bidiyon: Tauraron masoyin Ronaldo, Ishowspeed ya fashe da kuka bayan da Messi ya kafa tarihin zama wanda yafi yawan cin kwallaye a gasar World Cup

Kalli Bidiyon: Tauraron masoyin Ronaldo, Ishowspeed ya fashe da kuka bayan da Messi ya kafa tarihin zama wanda yafi yawan cin kwallaye a gasar World Cup

Duk Labarai
Tauraron masoyin Ronaldo watau Ishowspeed ya fashe da kuka bayan da lionel Messi yaci kwallo ta 17 a gasar cin kofin Duniya. wadda hakan ta bashi damar zama wanda yafi duk wani dan wasa a Tarihi yawan kwallaye a gasar. Bayan cin kwallon ta Messi, An ga Ishowspeed yana zubar da hawaye. https://twitter.com/i/status/2069113778113835272
Kalli Bidiyon: Kayatacciyar kwallon Messi inda ya zama na daya a Duniya wajan yawan cin kwallaye a Kofin Duniya

Kalli Bidiyon: Kayatacciyar kwallon Messi inda ya zama na daya a Duniya wajan yawan cin kwallaye a Kofin Duniya

Duk Labarai
Lionel Messi ya ci kwallo a wasan su da kasar Austria na gasar cin kofin Duniya watau World Cup. Wannan kayatacciyar kwallon da yaci itace ta 17 da yaci wadda kuma hakan ya bashi damar zama dan kwallon da yafi yawan kwallaye a gasar cin kofin Duniyar a Tarihi. A tarihin gasar cin kofin Duniya, ga wadanda suka fi yawan kwallaye kamar haka: 17 — Lionel Messi 16 — Miroslav Klose 15 — Ronaldo 14 — Gerd Müller 14 — Kylian Mbappé https://twitter.com/i/status/2069118298143302099