Friday, January 9
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma APC

Da Duminsa: Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma APC

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma jam'iyyar APC. Ya bayyana cewa wadanda suka baiwa Abba shawarar komawa jam'iyyar APC, ya kamata su kuma bashi shawarar ajiye mukamin gwamna tunda a jam'iyyar NNPP ya sameshi. Kwankwaso yace ji yake kamar a mafarki yake game da maganar komawar Abba jam'iyyar APC. Ya kuma karyata rade-radin da ake cewa wai hada baki suka yi da Abba.
”Yan Kudu da yawa na cewa wai tsoron kasar Amurka yasa Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya goge duk wata suka da yawa kasar Amurka a kafafen sada zumunta

”Yan Kudu da yawa na cewa wai tsoron kasar Amurka yasa Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya goge duk wata suka da yawa kasar Amurka a kafafen sada zumunta

Duk Labarai
'Yan kudu da yawa ne ke ta yayata cewa wai Malamin Addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya gog duk wani rubutu da yayi na sukar shugaban kasar Amurka. A cewarsu hakan na zuwane bayan matakij da shugaban Amurka, Donald Trump ya dauka akan kasar Venezuela. Sun bayyana cewa, wai tsoro ne ya kama malamin.
An zargi Bukola Saraki da Munafurci inda yake nuna yana PDP amma yana zagayawa ya ga Shugaba Tinubu

An zargi Bukola Saraki da Munafurci inda yake nuna yana PDP amma yana zagayawa ya ga Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta zargi tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki da cewa, yana Adawa a jihar Ta Kwara amma yana zagayawa ya rika ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Me magana da yawun jam'iyyar APC na jihar Kwara, Abdulwaheed Babatunde ne ya bayyana hakan, inda yace ya kamata Bukola Saraki ya fito ya gayawa mabiyansa bangaren da yake. Yace a Kwara sai ya nuna shi dan PDP ne amma sai ya rika zuwa Abuja yana ganawa da shugaba Tinubu.
Kalli Bidiyon: Kwankwaso ya bayyana cewa suna magana da wata jam’iyyar da yake son komawa amma ya saka musu sharadin sai sun bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa

Kalli Bidiyon: Kwankwaso ya bayyana cewa suna magana da wata jam’iyyar da yake son komawa amma ya saka musu sharadin sai sun bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, suna magana da wata jam'iyya inda yace zai koma cikinta. Yace amma ya saka musu sharadin sai in sun yadda zasu bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi a gidansa na 'yan Kwankwasiyya a Kano. Saidai bai bayyana sunan jam'iyyar ba. https://twitter.com/i/status/2007548263520669734 A baya dai, Hutudole ya ruwaito muku da Thisday cewa, jam'iyyar ADC ce Kwankwaso ke shirin komawa.
Kalli Bidiyon: Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Jankunne ta yi gargadin a daina Zhaghin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Kalli Bidiyon: Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Jankunne ta yi gargadin a daina Zhaghin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai
Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Jan Kunne ta gargadi masu zagin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da su daina. Ta yi wannan maganane akan shirin komawar gwamnan zuwa jam'iyyar APC. Tace babu yanda za'a yi a raba tsakanin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso. https://www.tiktok.com/@maryamabubakar24/video/7591086809044536632?_t=ZS-92lsJNKQtOK&_r=1
Kalli Bidiyon: Bayani dalla-dalla kan dalilin da yasa aka kama Khalifa Sani Zaria

Kalli Bidiyon: Bayani dalla-dalla kan dalilin da yasa aka kama Khalifa Sani Zaria

Duk Labarai
Daya daga cikin daliban malamin Addinin Islama Sheikh Khalifa Sani Zaria da aka kama ya fito yayi bayani dalla-dalla kan dalilin da yasa aka kamashi. Yace Addu'a ce aka baiwa malam yayi, shine aka biyashi, wai shine aka kamashi dalilin kudin da aka bashi. Yace ina 'yan siyasa da suke satar kudade da yawa? Yace kuma shin laifin malam ne dan yayi addu'a an bashi kudi? Kalli Bidiyon jawabin a comment. https://www.tiktok.com/@yushauyahaya1998/video/7590877679688109330?_t=ZS-92ledgevc9I&_r=1
Ba za’a dauke wuta ba ko so daya a shekarar 2026>>Ministan Wutar Lantarki ya bayar da tabbaci

Ba za’a dauke wuta ba ko so daya a shekarar 2026>>Ministan Wutar Lantarki ya bayar da tabbaci

Duk Labarai
Ministan wutar lantarki, Mr Adebayo Adelabu ya bayar da tabbacin samar da tsayayyar wutar Lantarki a shekarar 2026. Me baiwa ministan Shawara game da sadarwa da hulda da jama'a, Mr Bolaji Tunji. Ne ya bayyana hakan ranar Juma'a a wata sanarwa da ya fitar. Yace hakan na kunshene a cikin sakon sabuwar Shekara inda yace Gwamnati zata mayar da hankali wajan samar da tsayayyar wutar lantarki ga gidaje da masana'antu.
An fara cirewa ‘yan Najeriya Haraji: Ji yanda wata mata ke kuka bayan da aka cire mata harajin Naira 487,500

An fara cirewa ‘yan Najeriya Haraji: Ji yanda wata mata ke kuka bayan da aka cire mata harajin Naira 487,500

Duk Labarai
Wata mata shahararriya a kafafen sadarwa me suna Raye ta koka da cewa an cire mata harajin naira 487,500 bayan da ta kashe Naira Miliyan 6.5 wajan sayayya. Wannan koke nata na zuwane kwanaki kadan bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za'a fara cirewa mutane Haraji ranar 1 ga watan Janairu. Ta wallafa rasit din harajin da aka cire mata wanda ya dauki hankula sosai. Da yawan 'yan Najeriya dai na ta kokawa da maganar Harajin da Gwamnatin tarayya ta kawo.