Saturday, June 27
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Yanda Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya kira wani dan Tiktok ya yi masa zagin cin mutunci saboda yace a daina kallon Fim dinsa tunda basu da kishin Yankinsu

Kalli Bidiyon: Yanda Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya kira wani dan Tiktok ya yi masa zagin cin mutunci saboda yace a daina kallon Fim dinsa tunda basu da kishin Yankinsu

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya kira wani dan Tiktok inda yace ya ,zageshi. An ji a muryar da dan Tiktok din ya saka Lawal Ahmad na cewa me ya masa sannan suka kare da zagin Juna. Dan Tiktok din dai ya bayyana cewa saboda Bidiyon da yayi ne yace kar a kalli Fim din Lawal Ahmad shiyasa dan fim din ya kirashi yana zagi. https://www.tiktok.com/@yusufzango/video/7651650742679391506?_r=1&_t=ZS-97F3rHAsHsW
Kalli Bidiyon: Irin kokarin da golan Cape Verde yayi a wasansu da Spain

Kalli Bidiyon: Irin kokarin da golan Cape Verde yayi a wasansu da Spain

Duk Labarai
Golan Cape Verde, Vozinha duda yana dan shekaru 40 yayi kokari sosai a wasansu da kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain a gasar cin kofin Duniya da ake Bugawa a kasar Amirka. Golan na ta shan yabo saboda yawan kwallayen daya tare. Hakanan Kasar ta Cape Verde wanda wannan shine wasanta na World Cup na farko a Tarihi, ta bayar da mamaki saboda yanda suka rike Spain suka yi draw. https://twitter.com/i/status/2066592861647520170 https://twitter.com/i/status/2066582301757116532
Kalli Bidiyon: An hango Dala $600,000 a wallet din Ahmad XM, watau Sama da Naira Miliyan dari takwas kenan

Kalli Bidiyon: An hango Dala $600,000 a wallet din Ahmad XM, watau Sama da Naira Miliyan dari takwas kenan

Duk Labarai
Ahmad XM ya wallafa ribar da ya samu ta dala $82,000 watau kusan Naira Miliyan 110,kenan a trading din Bitcoin da yayi. Saidai a yayin da yake nuna ribar tasa, an kuma hango balance din wallet dinsa inda aka ga dala $600,000 watau sama da Naira Miliyan 800,000 kenan. Da yawa sun yi mamakin cewa yana da wannan kudin inda akai ta sharhi akai. https://www.tiktok.com/@ahmed_xm_/video/7651555564861918485?_r=1&_t=ZS-97EjJuxGv6v
Kalli Bidiyon: Da gaske Hadiza Gabon ta yi martani bayan zargin soyayya da Saleem Goje?

Kalli Bidiyon: Da gaske Hadiza Gabon ta yi martani bayan zargin soyayya da Saleem Goje?

Duk Labarai
Bidiyo na ta yawo a kafafen sada zumunta inda akw rade-radin cewa, wai Hadiza Gabon ta yi martani bayan zargin da matar Saleem Goje ta yi cewa yana soyayya da ita. Wani Bidiyo daya nuna Hadiza Gabon na kame-kame ya karade kafafen sadarwa inda ake cewa wai shine na martanin Hadizar. Saidai Bincike da Hutudole yayi ya gano cewa ba gaskiya bane, Har yanzu, Hadiza Gabon bata yi martani ba kan wannan zargi da aka mata. Hasali ma tun bayan bayyanar labarin, Hadiza bata kara yin wallafa a shafinta na sada zumunta ba. https://www.tiktok.com/@northysite/video/7651661404319124757?_r=1&_t=ZS-97Ei8vPsFXN
Kalli Bidiyon: Yanda Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake gurfana a gaban kotu

Kalli Bidiyon: Yanda Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake gurfana a gaban kotu

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake Gurfana a gaban kotu a yau Litinin inda ake ci gaba da shari'ar kan zarginsa da almundahanar kudaden jihar lokacin yana kan mulki. Kamar dai kullun, Jami'an tsaro sun tare hanyoyin dake kaiwa zuwa kotun da akewa malam Shari'a. Saidai a zaman na yau, Sauran mutane 2 da ake musu shari'a tare da malam Nasiru Ahmad El-Rufai basu samu halartar zaman kotun ba wanda hakan yasa kotun ta daga zaman zuwa Ranar 24 ga watan Yuni. https://twitter.com/i/status/2066471231075819719
Kotu ta bukaci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC

Kotu ta bukaci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta bukaci hukumar zabe me zaman kanta data soke rijistar jam'iyyar ADC. Kotun ta dauki wannan hukunci ne bayan da wasu 'yan kishin kasa suka shigar da kara inda suke bukatar a soke rijistar jam'iyyun siyasa 5 ciki hadda ADC ,sauran sune Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP), da Zenith Labour Party (ZLP). Masu shigar da kara sun bayyana cewa, jam'iyyun sun kasa cika sharudan da ake bukata na kasancewar jam'iyyar siyasa,. Sharudan sune kowace jam'iyya akalla ta yi nasarar kaso 25 a zaben shugaban kasa daga kowace jiha, ko kuma ya zamana tana da zababben dan siyasa a matakin kasa, Jiha ko karamar hukuma. Saidai suka wadancan jam'iyyun basu cika wadannan sharudan ba. Masu shigar da karar sun bukaci cewa, kotu ta tabb...