Thursday, July 9
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: A akidar Ahlussunah da kuma koyarwar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) babubinda akace talakawa su dumama Shuwagabannin, kamar yanda Sheikh Salihu Zaria ke cewa>>Inji Dr. Jamilu Aliyu

Malam Dr. Jamilu Aliyu ya bayyana cewa yana tare da Sheikh Salihu zaria game da kin biyan Haraji da gwamnati ke kokarin sakawa Talakawa Saidai yace baya tare da Malam Salihu Zaria akan cewa wai a Dumama 'yan Majalisa, yace ba koyarwa lr Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) bace dumama shuwagabanni. Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi umarni da a yi hakuri idan aka samu shuwagabanni marasa adalci. Malam kuma yace wasa yayi yawa a wa'azin Sheikh Salihu Zaria inda yace ya kamata ya gyara. https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7590329793590152468?_t=ZS-92huS6g5bNp&_r=1
Kalli Bidiyon: Bayan da Rahama Saidu ta wallafa wannan Bidiyon da ya jawo cece-kuce sosai, wata tace mata, wata Tace mata “Nòwnùwà sun yi kyau, Allah kawo Kasuwa”

Kalli Bidiyon: Bayan da Rahama Saidu ta wallafa wannan Bidiyon da ya jawo cece-kuce sosai, wata tace mata, wata Tace mata “Nòwnùwà sun yi kyau, Allah kawo Kasuwa”

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta wallafa Bidiyo wanda ya dauki hankula sosai a shafinta na Tiktok. Wata ta mata comment cewa, Nonuwa sun yi kyau, Allah kawo Kasuwa. Saidai abin baiwa Rahama Saidu dadi ba inda ta mayar mata da martani me zafi. https://www.tiktok.com/@rahamasaidu2/video/7590092459124772114?_t=ZS-92hrmmNoPHk&_r=1
Da Duminsa: Rahotanni sun ce wasu da ba’a san ko su wanene ba sun Afkawa Sheikh Salihu Zaria biyo bayan maganar da yayi kan cewa ba za’a biya kudin Haraji ba

Da Duminsa: Rahotanni sun ce wasu da ba’a san ko su wanene ba sun Afkawa Sheikh Salihu Zaria biyo bayan maganar da yayi kan cewa ba za’a biya kudin Haraji ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ba'a san ko su wanene ba sun Afkawa Malam Sheikh Salihu Zaria biyo bayan cewa da yayi ba za'a biya kudin Haraji ba. Sheikh Salihu Zaria dai yace duk wanda ya zo karbar Haraji a wajan Talakawa zai dandana kudarsa. A cewa wanda ya kawo Rahotanni yace an kaiwa malam farmakinne dalilin wannan wa'azi da yayi. https://www.tiktok.com/@ib_danfilm01/video/7590153453876301086?_t=ZS-92honfTPePw&_r=1
Allah Sarki Duniya, Abokan Anthony Joshua sun zo Najeriya da kafafunsu, gashi yanzu za’a mayar dasu kasashensu a akwatunan Gawa

Allah Sarki Duniya, Abokan Anthony Joshua sun zo Najeriya da kafafunsu, gashi yanzu za’a mayar dasu kasashensu a akwatunan Gawa

Duk Labarai
An tafi da gawar Abokan dan damben Najeriya, Anthony Joshua zuwa kasashensu. Abokan Anthony Joshua su biyu ne suka rasa rayukansu a Hadarin motar da ya rutsa das a kan hanyar Legas zuwa Ibadan. Shi kuma Anthony Joshua ya ji raunuka aka kwantar dashi a Asibiti amma ya ji sauki an sallameshi. https://twitter.com/Cleverlydey4u/status/2006622653919146317?t=9mfXxwQKg-_NWaE2-bQcXA&s=19
Ana Rade-radin cewa, Akwai yiyuwar shugaba Tinubu ya dauki Shugaban jam’iyyar APC amatsayin mataimaki a 2027

Ana Rade-radin cewa, Akwai yiyuwar shugaba Tinubu ya dauki Shugaban jam’iyyar APC amatsayin mataimaki a 2027

Duk Labarai
Rade-radi na yawo a kafafen sada zumunta cewa, akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai dauki Shugaban jam'iyyar APC a matsayin mataimakinsa a 2027. A baya dai an ta yada cewa, Tinubu zai dauki wani wanda ba Kashim Shettima ba a matsayin mataimakinsa a zaben 2027. https://twitter.com/Pharmacio001/status/2006390423208480984?t=KPEcFr0W1vB0CfLcxTxopA&s=19
Allah Sarki: Da Misalin Karfe 2 na dare mahaifiyata ta rigamu gidan gaskiya>>Inji Golan Super Eagles, Stanley Nwabali

Allah Sarki: Da Misalin Karfe 2 na dare mahaifiyata ta rigamu gidan gaskiya>>Inji Golan Super Eagles, Stanley Nwabali

Duk Labarai
Golan Super Eagles, Stanley Nwabali ya bayyana cewa, da misalin karfe 2 na dare, Mahaifiyarsa ta rigamu gidan gaskiya. Yace kuma dama mahaifinsa bai wece wata 2 da rasuwa ba Yace ji yake kamar karya daina buga Kwallon saboda ba dadi. https://twitter.com/DAMIADENUGA/status/2006449271948849440?t=fYaMTaXPRVe1T4W_T6kZ1g&s=19
Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan kasar Ghana sun kama Fastonnan da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan kasar Ghana sun kama Fastonnan da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa, Hukumar 'yansandan kasar sun kama fastonnan me suna Evans Eshun da yace wai za'a yi tashin Qiyama ranar 25 ga watan Disamba, watau ranar Kirsimeti. Hukumar 'yansandan ta ce bata yadda da masu amfani da addini suna tayarwa da mutane hankali ba inda tace tabbas an kama Fasto Evans Noah. Saidai bata bayyana laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba. Fasto Evans Noah yace wai an masa wahayin za'a yi tashin Qiyama ranar 25 watan Disamba sannan an bashi Umarnin sassaqa jirgin ruwa irin na Annabi Nuhu saboda wai za'a yi ruwan sama. Saidai daga baya da ranar Kirsimeti ta zo ba'a yi tashin qiyamar ba, ya bayyana cewa shi ranar kawai aka sanar dashi, ba'a sanar dashi shekarar da za'a yi tashin qiyamar ba.