Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Akwai matsala a sakamakon da muka saki, WAEC tace dalibai su sake duba sakamakon jarabawarsu a yau

Akwai matsala a sakamakon da muka saki, WAEC tace dalibai su sake duba sakamakon jarabawarsu a yau

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta WAEC ta bayyana cewa, akwai tangarda a sakamakon data saki a farko. Dan haka ne ta dakatar da duba sakamakon inda tace a ranar Juma'a dalibai su sake duba sakamakon jarabawarsu. Hukumar ta sanar da hakanne ta bakin me kula da hulda da jama'ar ta, Moyosola Adesina. Bayan sakin sakamakon farko, an samu korafi daga iyaye ka yawan faduwar da aka yi jarabawar ta bana inda har wasu ke kiran a soke jarabawar ta bana.
Kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa saboda rashin wuraren adana – NAFDAC

Kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa saboda rashin wuraren adana – NAFDAC

Duk Labarai
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta ce kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa ne sakamakon rashin wuraren adana abinci da suka dace. Darakta-janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels, inda ta ce wuraren adana abinci sun yi kaɗan a ƙasar. Ta ce idan aka samu wuraren adana abinci masu kyau, dangin abinci irin ganyayyaki da su tumatiri duka ba za su ci gaba da lalacewa ba. Ta ce hakan ne ya sa suke ɗuakar matakai na ganin abinci da ake adanawa sun ɗauki lokaci ba su lalace ba ta hanyar samar da wuraren adana na zamani.
Atiku ya bukaci a saki Sowore

Atiku ya bukaci a saki Sowore

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi Alla-wadai da kamawa tare da tsare fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore. Atiku ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido na sufeto janar na ƴansandanƙasar suka yi wa Sowore. "Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ba ya cikin ka'ida. Dole ne a yi tur da batun," in ji Atiku. Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin adalci da kuma kyayyawar shugabanci da ake yi a Nijeriya. Wasu rahotanni ma na bayyana cewa an lakaɗawa Sowore duka har ma ƙarya masa hannu, inda ake zargin ƴansanda da aikatawa. Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴansanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai bane, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Najeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi ga...
An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026

An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026

Duk Labarai
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa an kayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026. NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar - don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin. Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara. Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Najeriya - inda...
Sam babu Adalci: Soja ya soki shugaba Tinubu saboda baiwa ‘yan kwallo kyautar Naira Miliyan 50 inda ya nuna dakunan bukka da suke kwana a ciki a daji

Sam babu Adalci: Soja ya soki shugaba Tinubu saboda baiwa ‘yan kwallo kyautar Naira Miliyan 50 inda ya nuna dakunan bukka da suke kwana a ciki a daji

Duk Labarai
Sojan Najeriya ya koka da rashin adalci bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa 'yan kwallo mata kyautar Naira Miliyan 150. Sojan yace albashinsu dubu dari ne inda ya nuna dakunan bukka da suke kwana yace sam babu adalci a lamarin. https://twitter.com/oxygist/status/1953465690469335432?t=m-z8alJwI3WyQpQeoP7o4w&s=19
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Mahaifin dan Bello ya rigamu gidan Gaskiya

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Mahaifin dan Bello ya rigamu gidan Gaskiya

Duk Labarai
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Allah Ya Yiwa Mahaifin Bello Galadanci (Ɗan Bello) Malam Habib Rãșuwa yanzun nan. Allah ya gafarta masa.
Kalli Bidiyon: Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba sai idan ya yadda ya fara zama mataimakin shugaban kasa>>inji Fasto Ayodele

Kalli Bidiyon: Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba sai idan ya yadda ya fara zama mataimakin shugaban kasa>>inji Fasto Ayodele

Duk Labarai
Fasto Ayodele ya bayyana cewa, Peter Obi idan ba hakuri yayi ya zama mataimakin shugaban kasa ba, ba zai taba zama shugaban kasa ba. Hakanan yace shima Nuhu Ribadu sai ya koma Adamawa ya zama Gwamna kamin ya samu nasarar zama shugaban kasa, Saidai yace mutanen Adamawa basa son Nuhu Ribadu dan haka ba zai iya nasarar zama Gwamna ba. https://twitter.com/OneJoblessBoy/status/1953228051803771334?t=3i79lIQ384uaiDguu3btjg&s=19 Peter Obi dai shine yayi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a jam'iyyar Labour party inda ya zo na 3. Hakanan Nuhu Ribadu ana rade-radin shine zai yi takara a APC idan Tinubu ya kammala wa'adinsa na shekaru 8.
Fitsari a tsaye Halal ne, Kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi, Kuma ka karyata ka Mùtù ka shiga jahannama>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Fitsari a tsaye Halal ne, Kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi, Kuma ka karyata ka Mùtù ka shiga jahannama>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Malam Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, Fitsari a tsaye halal ne. Malam ya kara da cewa an ruwaito a Hadisi kuma sun yadda. Yace mutum ya karyata ya mutu ya shiga wuta. https://www.tiktok.com/@wazirinfaira/video/7534807105774112006?_t=ZS-8ygUd5VEYvR&_r=1 Saidai da yawa 'yan darika basu yadda da wannan magana ba.
Kalli Bidiyo: Shekara daya kenan da wani dan fim Ali Nuhu ya fito ya tafka Babbar Shirka yana cewa, Wai Annabi(SAW) ya Ceceshi>>Inji Baffa Hotoro

Kalli Bidiyo: Shekara daya kenan da wani dan fim Ali Nuhu ya fito ya tafka Babbar Shirka yana cewa, Wai Annabi(SAW) ya Ceceshi>>Inji Baffa Hotoro

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Baffa Hotoro ya bayyana cewa, Shekara daya kenan da Ali Nuhu ya fito yana waka yana baiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) matsayin Allah. Yace hakan shirka ne. Malamin ya bayyana hakane yayin da yake wa'azi. https://www.tiktok.com/@jrbunza/video/7535782654730341638?_t=ZS-8ygRbS946Tp&_r=1