Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki

ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki

Duk Labarai
ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki …samun matashi irin Hon. Muhammad Sulai Yaro abu ne mai wuya Tabbas samun matashi kamar Hon Muhammed Sulai Yaro wanda aka nada shi a matsayin Dan Gatan Girei abu ne da kamar wuya, matashi ne da ya mayar da hankalin sa kan takalawa. A jiya ne dai ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa, inda ya debi yara marayu sama da dari biyu ya yi musu sabon dinki, kuma ya hada musu liyafa, har saida ya zubar da hawaye a wajen. Haka kuma ya yi musu alkawari zai ci gaba da tallafa musu har karshen rayuwar su. Wace fata za ku yi masa? Daga Hon Ishaq B Aliyu
Wata Sabuwa: Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai dakko Matthew Hassan Kuka ko Yakubu Dogara ya mai mataimaki a 2027

Wata Sabuwa: Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai dakko Matthew Hassan Kuka ko Yakubu Dogara ya mai mataimaki a 2027

Duk Labarai
Dan Gwagwarmaya, Mahadi Shehu ya bayyana mutanen da yake tsammanin zasu yi takara a zaben shekarar 2027 da abokan takararsu. Ya rubuta hakane a shafinsa na X inda ya bayyana 'yan takarar da yake tsammanin zasu yi takara a kowacw jam'iyya. A jam'iyyar APC yace akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi takara da tsohon gwamnan jihar Borno, Modu Ali Sheriff, ko Yakubu Dogara, ko babban Fasto, Mathew Hassan Kuka. A jam'iyyar ADC kuwa, yace akwai yiyuwar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ne zasu yi takara a 2027. A Labour Party kuwa yace Peter Obi da Ko dai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Datti Baba Ahmad, ko Aminu Waziri Tambuwal. A PDP kuwa yace akwai yiyuwar, Goodluck Jonathan su yi takara tare da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ko ya dau...
Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar Tinubu ya roki ‘yan Arewa

Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar Tinubu ya roki ‘yan Arewa

Duk Labarai
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya roki 'yan arewa da su sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Yayi wannan rokone a yayin wani taro da ya shirya na tsaffin 'yan majalisar tarayya a Abuja. Ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu Tinibu ba shugaban kudancin Najeriya bane kadai, shugaba ne na kowanne yanki. Yace ko dan Tinubu ya kammala ayyukan ci gaban da ya ke yi a Arewa, ya kamata ace 'yan Arewan su sake zabensa.
Da Duminsa: Gini me hawa 3 ya fadi a Abuja

Da Duminsa: Gini me hawa 3 ya fadi a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga Abuja na cewa, gini me hawa 3 ya rushe a Life Camp da ammacin ranar Asabar. Tini 'yansanda suka je wajan aka killaceshi sannn hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta kai dauki. Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an ceto wani dan kasar Nijar a lamarin. Rahoton yace shi kadai ne lamarin ya rutsa dashi kuma an garzaya dashi asibitin Cedar Crest Hospital inda ake bashi kulawa.
Kabir Gombe Kazami ne, Kuma kwanannan shi da Sheikh Bala Lau suka kwacewa marayu makaranta a Gombe, aikinsu kenan zalintar marayu, Sheikh Musa Salihu Alburham da Wani malamin Izalan Jos suka soki Shugabancin Izala na kasa

Kabir Gombe Kazami ne, Kuma kwanannan shi da Sheikh Bala Lau suka kwacewa marayu makaranta a Gombe, aikinsu kenan zalintar marayu, Sheikh Musa Salihu Alburham da Wani malamin Izalan Jos suka soki Shugabancin Izala na kasa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin shugabancin Izala na kasa da Izalar Jos. A baya Sheikh Dr. Musa Salihu Alburham ya soki Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam inda har 'ya'yan malam suka mayar da martani. A yanzu kuma fadan ya kara fadada inda Wani daga cikin Malaman Izalar Jos ya fito ya zargi shugabancin Izala na kasa karkashin Jagorancin Sheikh Bala Lau da zalintar marayu. https://www.tiktok.com/@darul_burhan_majlis/video/7534101238833581318?_t=Z...
Arewa ba ta da hujjar zargiɲ Tinubu na nuna mata wariya -inji Gwamna Uba Sani

Arewa ba ta da hujjar zargiɲ Tinubu na nuna mata wariya -inji Gwamna Uba Sani

Duk Labarai
Arewa ba ta da hujjar zargiɲ Tinubu na nuna mata wariya -inji Gwamna Uba Sani Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Arewa ba ta da hujjar zargin Shugaba Bola Tinubu da nuna wariya. Ya bayyana cewa Arewa tana da muhimman mukamai a gwamnati kamar harkar noma da tsaro. Uba Sani ya kuma ce Jihar Kaduna ta samu ci gaba a fannin noma da zaman lafiya karkashin gwamnatin Tinubu, inda babu rikicin addini ko kabilanci a cikin shekaru biyu da suka gabata. Ayau News ta ruwaito Gwamnan ya bukaci shugabannin Arewa da su daina siyasantar da komai, su mayar da hankali kan aiki da cigaban al’umma. Me zaku ce?
Bidiyo: Itama Momi Gombe ta baiwa abokin aikinta, Jarumin Kannywood, Jamilu Kochila gudummawar Naira Miliyan 1 a waja bikin aurensa

Bidiyo: Itama Momi Gombe ta baiwa abokin aikinta, Jarumin Kannywood, Jamilu Kochila gudummawar Naira Miliyan 1 a waja bikin aurensa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Momi Gombe ta baiwa abokin aikinta, Jamilu Kochila gudummawar Naira Miliyan 1 a wajan bikinsa. https://www.tiktok.com/@agg_multimedia_services/video/7534126648350838072?_t=ZS-8yYx8vacpFp&_r=1 Itama Teema Makamashi ta baiwa Kochila gudummawar Naira 500,0000. Hakanan akwai da kasuwa da ya baiwa Angon gudummawar Naira Miliyan 10.
Kalli Bidiyon yanda Ahmed Musa ya baiwa Jarumin Kannywood, Jamilu Kochila Gudummawar Naira Miliyan 5 a ranar aurensa

Kalli Bidiyon yanda Ahmed Musa ya baiwa Jarumin Kannywood, Jamilu Kochila Gudummawar Naira Miliyan 5 a ranar aurensa

Duk Labarai
Shahararren dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya baiwa jarumin fina-finan Hausa, Jamilu Kochila gudummawar Naira Miliyan 5 a wajan bikin aurensa. Ahmed Musa wanda shine shugaban Kungiyar Kano Pillars ya samu rakiyar abokinsa, Shehu Abdullahi wajan bikin. https://www.tiktok.com/@agg_multimedia_services/video/7534121142206942470?_t=ZS-8yYuFXf1o8n&_r=1