Ku Yi Amfani da Shafukan Sada Zumunta Wajen Ƙarfafawa Ƙasa, Ba Raba Kan Jama’a Ba, Sakon Shugaba Tinubu Ga Matasa
Ku Yi Amfani da Shafukan Sada Zumunta Wajen Ƙarfafawa Ƙasa, Ba Raba Kan Jama’a Ba, Sakon Shugaba Tinubu Ga Matasa.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya da ke da tasiri a kafofin sadarwar zamani da su yi amfani da wannan damar wajen haɗa kan al’umma da ƙarfafa cigaban ƙasa. Ya jaddada muhimmancin tantance gaskiyar bayanai kafin yada su, yana mai cewa karfin da kafafen ke da shi na da tasiri a fagen cigaba da haɗin kai haka kuma amfani da su ta mummunar hanya na iya haifar da rikici.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron Progressives Digital Media Summit da aka gudanar a Abuja, mai taken “Unveiling the Critical Role of New Media in National Development.” Ya ce matasa sun fara nuna kwarewa ta hanyar kirkire-kirkire da amfani da fasahar zamani do...








