Friday, February 27
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Wasannan na Mari da ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya

Kalli Bidiyo: Wasannan na Mari da ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya

Duk Labarai
Wasan Mari da mafi yawanci ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya. Wasan wanda har ana saka kyauta ga wanda yafi iya yin marin an ganshi an fara yinshi a Najeriya. Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki sosai inda ake ta muhawara akai. https://twitter.com/AsakyGRN/status/1975275774308663458?t=zMzci2-c8sk72ZCDflhcJw&s=19 Tuni dai wani malamin Addinin Islama ya jawo hankalin Musulmai da cewa wasan bai halasta ba a Musulunci kuma su gujeshi. https://twitter.com/IdrisAOni1/status/1975585618076774801?t=JQQfXTWH2WuPWr4dwZuinw&s=19
Kudi sun yi yawa a hannun mutane, Kuma na ji dadin matakan da CBN ya dauka wajan rage yawan kudaden dake hannun mutane>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Kudi sun yi yawa a hannun mutane, Kuma na ji dadin matakan da CBN ya dauka wajan rage yawan kudaden dake hannun mutane>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Duk Labarai
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana jin dadinsa game da matakan da babban bankin Najeriya CBN ya dauka wajan magance yawan kudi a hannun mutane. Sarki Sanusi yace hakan yasa hauhawar farashin kayan abinci ya ragu duk da dai har yanzu yana kan maki 20 wanda yayi yawa. Sarkin yace tattalin arzikin Najeriya ya dawo daga hanyar rugujewa da ya dauka saboda wanan mataki da CBN ya daka. https://twitter.com/KanEmirateMedia/status/1975645093714665940?t=wj0dZ4XwsPxOAD9AaX2o3A&s=19
Kalli Bidiyo: Wallahi da wadanda ba musulmai bane suka yi irin wannan Kalamai akan Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Musulmai sun turasu Qiyama>>Inji Farfesa Ibrahim Maqari

Kalli Bidiyo: Wallahi da wadanda ba musulmai bane suka yi irin wannan Kalamai akan Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Musulmai sun turasu Qiyama>>Inji Farfesa Ibrahim Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Ya bayyana cewa, da wadanda ba musulmai bane suka yi kalamai na taba Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace da tuni hakan ya kawo tashin hankali. Malam yace "Da Tuni an fara Qone-Qone da an fhille Mhusu Khawuna. Yace amma wadanda suke kiran kansu musulmai ne ke irin wannan abin. Malam ya bayyana hakane cikin sheshekar kuka a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai. https://www.tiktok.com/@hassan.a.hassan.2/video/7557739024941600011?_t=ZS-90N9J038S1p&_r=1
Ina mamakin yanda ake mana Qazafin wai muna Lalata da Mhata, Saboda matan dake bin mu mun yi ‘ya’ya da jikoki dasu>>Inji Tanimu Akawu

Ina mamakin yanda ake mana Qazafin wai muna Lalata da Mhata, Saboda matan dake bin mu mun yi ‘ya’ya da jikoki dasu>>Inji Tanimu Akawu

Duk Labarai
Tauraron Fina-finan Hausa, Tanimu akawu ya bayyana cewa, Abin na bashi mamaki wai da ake musu Qazafin cewa, suna lalata da mata. Yace yawanci matan dake binsu sun yi 'ya'ya da jikoki dasu. Yace dan fim me taimako ne inda yace shi kanshi ya aurar da yaran mutane 2. https://www.tiktok.com/@abdulsauty1/video/7558205933583617298?_t=ZS-90N7paOSItN&_r=1 Tanimu Akawu ya kawo misalin yanda wata yarinya bafulatana da akawa auren dole ta gudo ta sameshi tace tana son shiga film inda yace sai da ya kira iyayenta. Yace da Kano ta je da an lalata mata rayuwa.
”Yan Kasuwar Abuja na kokawa da Harajin da ake karba daga hannunsu saboda sauraren Radiyo da kallin TV

”Yan Kasuwar Abuja na kokawa da Harajin da ake karba daga hannunsu saboda sauraren Radiyo da kallin TV

Duk Labarai
'Yan kasuwar Abuja na kokawa da karbar Harajin Kallon TV da sauraren Radio da ake karba daga hannunsu. Daya daga cikin 'yan kasuwar ne ya wallafa Rasit din karbar Harajin. Ya koka da cewa, ta yaya za'a ce mutum ya biya Haraji saboda kallon Talabijin da Sauraren Radio? https://twitter.com/humeeemk/status/1975284134525259814?t=0k_zHhvRF9Clmaoa_5l-sQ&s=19
Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya ya yi murabus kan zarginsa da amfani da digirin bogi

Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya ya yi murabus kan zarginsa da amfani da digirin bogi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Geoffrey Uche Nnaji. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin ministan, wanda ya biyo bayan zarginsa da aka yi da amfani da digirin bogi. An dai zargi tsohon minista ne da amfani da digirin bogi daga Jami'ar Najeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin ƴan ƙasar matuƙa, duk da ya musanta. Njaji ya ce ana masa bita da ƙulli ne, lamarin da ya zargi "abokan hamayyarsa a siyasa" da yunƙurin ɓata masa suna. Tinubu ya yi godiya a gare shi "bisa hidimta wa Najariya" sannan ya yi masa fatan alheri.
Kalli Bidiyon: A tabbatar malaman da aka gayyato zasu yiwa Malam Lawal Triumph Tambayoyi sun san Hadisi da Qur’ani sosai, idan ba haka ba zamu ji Kunya>>Inji Dan Darika Umar

Kalli Bidiyon: A tabbatar malaman da aka gayyato zasu yiwa Malam Lawal Triumph Tambayoyi sun san Hadisi da Qur’ani sosai, idan ba haka ba zamu ji Kunya>>Inji Dan Darika Umar

Duk Labarai
Dan Darika, Umar ya bayyana damuwa da kuma gargadi kan cewa ya kamata a ce an samu malamai wanda suka san Qur'ani da kuma Hadisi su zaina da malam Lawal Triumph. Umar yayi gargadin cewa, idan ba'a samu malamai masu ilimi ba, za'a iya jin kunya. Ya bayyana cewa ya san Malam Lawal Triumph sosai. https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7557750978754202898?_t=ZS-90LupEEOg53&_r=1