An ga Matar Rarara ta 3 a bainar jama'a inda aka ga suna daukar hotuna tare.
Wasu dai na kusa dashi sun rika bayyana cewa itace dama bata son ana daukar ta hoto.
Kalli Bidiyon anan
Sojan Najeriya ya bayyana cewa masu kiran a kori Sojan ruwa, AM. Yerima daga aiki, su jira su ga abinda zai faru idan hakan ta faru.
Yace ba zai yiyu Janar ya bayar da umarni ba wani Dan siyasa yace kada abi wannan umarnin ba.
https://twitter.com/General_Somto/status/1989027173659730321?t=ocG686SlrNHmBopm3mhWdQ&s=19
Hakan na zuwane bayan dambarwar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa, AM. Yerima bayan da sojan ya hana Wike Shiga wani fili a Abuja.
Wannan Bidiyon na wani dan siyasa daga Arewa da ya tara kudi za rabawa Talakawansa ya dauki hankula saboda yawan kudin.
Wasu daga kudu sun rika tambayar ko mutanen Arewa na da Injin Buga kudi ne?
https://twitter.com/dammiedammie35/status/1989434808951574534?t=WBIQ9YBlo1B4NWGAe2KiIQ&s=19
Wannan matashiyar ta bayyana cewa tana neman a samu wani ya aureta.
Inda tace waa bukata ce ta taso mata da gaggawa inda tace bayan auren zata yi bayani.
https://twitter.com/Oummiih/status/1989206912865317172?t=1RyZq2FseqNLlst-z-OPpw&s=19
Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo ya mayarwa da Sheikh Dr. Ahmad Gumi da martanin cewa da gaske an binne Kiristoci da yawa wanda ake zargin 'yan Bindiga da kashewa.
Hakan na zuwane bayan da Rahotanni suka bayyana cewa, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya zargi Kiristoci da binne akwatunan gawa a karya da babu gawar a ciki dan su nuna cewa, an kashe musu mutane.
Faston ya kai ziyara wani kabari da aka binne mutane 27 kamar yanda yace inda anan ne yace zasu sa matasa su hako gawarwakin dan a nuna shaida.
A cikin jawabinsa ne yake cewa Addinin Musulunci addinin Qarya, Subhanallah.
Saidai wasu hadda Kiristoci sun bayyana cewa abinda ya fada bai kamata ba, bai kamata bacin ran abinda Sheikh Gumi ya masa ba yasa ya bayyana gaba dayan Addinin Musulunci da addinin Qarya ba.
https://tw...
Hadimar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai zarce a shekarar 2027 ba.
Tace tana daga cikin wadanda suka zabi Tinubu amma ta yi nadamar zabenshi.
Lauretta Onochie dai ta dade tana sukar Gwaamnatin Shugaba Tinubu dan haka wadannan kalamai nata ba zasu zowa mutane da mamaki ba
Wasu Kiristocin Najeriya sun fito zanga-zanga inda suka nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gaggauta kawo musu daukin da ya musu Alkawarin kawowa.
Tsohon dansandan Najeriya, Sunny Anyanwu ya gabatar da Naira dubu 5 daga cikin dubu 49 da yake karba a matsayin kudin fansho ga sojan ruwa AM. Yerima.
Dansandan yace a aika masa da lambar asusun banki na Soja Yerima dan ya aika masa da kudin.
yace abinda sojan ruwan yawa Wike abin a yaba ne inda yace yana fatan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai baiwa sojan lambar yabo.
Turmutsutsu a gidan karamin ministan tsaro dake Gusau jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi sanadiyyar rasa rai daya wasu mutane 6 suka jikkata da yammacin ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 7:30 na ranar Alhamis yayin da mutane suka taru a gidan nasa dan tarbarshi.
Zagazola Makama yace wanda ya rasun sunansa, Khalifa Uzairu kuma dan kimanin shekaru 23 ne.
Sannan akwai mutane 6 Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu, da Inusa Musa Shehu da su kuma suka jikkata suna karbar magani.
An kai jami'an tsaro wajan sannan an fara binciken yanda lamarin ya faru.
Wata tsohuwar malamar Jinya, Nurse ta dauki hankula saboda irin bayanan data fitar kan irin yanda ta gudanar da aikinta.
Tace wasu lokutan sukan canjawa me Jego Jariri ko kuma su dauke jariri me rai su ajiye matacce.
Tace suna sayar da Namijin Jariri akan Naira Miliyan 4.5 ko Miliyan 3. Hakanan sukan sayar da macen Jaririya akan Naira Miliyan 2.5.
https://twitter.com/instablog9ja/status/1989329219139051955?t=LzUAB8PG1hcsm4opoIK0ug&s=19