Saturday, February 28
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce Kwamishinan ‘yansandan Kanon ya basu kunya kuma suna Allah wadai da abinda yayi na kin Halartar Bikin ‘yancin Najeriya

Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce Kwamishinan ‘yansandan Kanon ya basu kunya kuma suna Allah wadai da abinda yayi na kin Halartar Bikin ‘yancin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi Allah wadai da kwamishinan 'yansandan jihar, Inda yace ya basu kunya saboda kin halartar bikin ranar 'yancin Najeriya. Gwamna Abba yace Kwamishinan ya dauki matakai da suka nuna cewa yana goyon bayan wata jam'iyya. Gwamnan yace shine Gwamna sannan shugaban tsaro na jihar Kano kuma Allah ne ya bashi, dan haka babu wanda ya isa ya kwace mai. Gwamnan yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya cire Kwamishinan 'yansandan daga jihar Kano na kawo musu wani. Kalli Jawabin Gwamnan a kasa: https://www.tiktok.com/@sardauna_shoot.ng/video/7556210141406711048?_t=ZS-90BmkqFaY76&_r=1
Daga yau, 1 ga watan Oktoba, hukumar shige da fici ta Najeriya zata fara kama ‘yan kasar waje dake zaune a Najeriya ba bisa ka’ida ba, ko wadanda suka shigo Najeriya ba tare da takardu ba

Daga yau, 1 ga watan Oktoba, hukumar shige da fici ta Najeriya zata fara kama ‘yan kasar waje dake zaune a Najeriya ba bisa ka’ida ba, ko wadanda suka shigo Najeriya ba tare da takardu ba

Duk Labarai
Rahotanni sun ce daga yau, 1 ga watan Oktoba, Hukumar kula da shige da fici ta Najeriya zasu fara kame da hukunta wadanda suka shigo Najeriya bizarsu ta kare basu fita ba da wadanda kuma suna shigo ba tare da takardu ba. Wadanda aka kama da laifi, zasu iya fuskantar hukuncin mayar dasu kasashensu ko kuma cinsu tara. Wanda aka kama ya dade a Najeriya tsawon watanni 3 bayan shigowa kuma takardunsa sun kare, zai biya tarar Dala $15 kullun. Ko kuma a bashi zabin hanashi shigowa Najeriya na tsawon shekaru 2. Sai kuma wadanda suka tsaya a Najeriya na tsawon watanni 3 zuwa shekara 1, su kuma za'a musu hukuncin biyan tarar dala $15 kullun ko kuma hanasu shigowa Najeriya na tsawon shekaru 5.
Kalli Bidiyo: Ta je Saudiyya tana rokon Allah ya hana Salisu Umar Salinga Kwanciyar Hankali har sai ya biya mahaifiyarta kudadenta

Kalli Bidiyo: Ta je Saudiyya tana rokon Allah ya hana Salisu Umar Salinga Kwanciyar Hankali har sai ya biya mahaifiyarta kudadenta

Duk Labarai
Wannan matashiyar ta je Saudiyya a dakin Ka'aba tana rokon Allah ya hana Salisu Umar Salinga Kwanciyar Hankali. Tace Allah ya hanashi abinda yake so har sai ya biya mahaifiyarta kudin ta dake hannunsa. Saidai da yawa sun bayyana cewa irin wannan addu'a da ta yi bata dace ba. https://www.tiktok.com/@realgudgirl0/video/7554450456676764936?_t=ZS-90BWkcIbgqO&_r=1
Karanta Jadawali: An fitar da bayanin Jihohin da dalibai suka fi karbar bashin karatu na NELFUND na Gwamnatin Tarayya

Karanta Jadawali: An fitar da bayanin Jihohin da dalibai suka fi karbar bashin karatu na NELFUND na Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, an fitar da bayanin jihohin da dalibai suka fi karbar Bashin Karatu na Gwamnatin Tarayya da ake kira da NELFUND. Jihohin sune kamar haka: 1. Borno: 61,3842. Kano: 57,9833. Kaduna: 45,0024. Katsina: 43,6025. Oyo: 33,2236. Bauchi:33,0277. Kwara: 31,6408. Plateau: 31,3149. Gombe: 31,30810. Taraba: 26,505
PENGASSAN ta amince ta janye yajin aiki bayan Dangote ya amince ya mayar da ma’aikata 800 da ya kora bakin aiki

PENGASSAN ta amince ta janye yajin aiki bayan Dangote ya amince ya mayar da ma’aikata 800 da ya kora bakin aiki

Duk Labarai
Ƙungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun saɓani da matatar mai ta Dangote Yajin aikin na zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma'aikata 800 saboda sun nuna sha'awar shiga ƙungiyar. Gwamnatin Najeriya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya. Cikin wata sanarwa da ma'aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma'aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita. "Babu ma'aikacin da zai cutu sakamakon saɓanin matatar Dangote da PENGASSAN," a cewar sanarwar. A nata ɓangare, ƙungiyar ta PENGASSAN ta ''amince ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin''. Tun bayan fara...
Kalli Bidiyo: Dan Allah duk wanda muka yi fada dashi, dan Darajar wannan dakin ya yafe min>>Inji Hassan Make-Up

Kalli Bidiyo: Dan Allah duk wanda muka yi fada dashi, dan Darajar wannan dakin ya yafe min>>Inji Hassan Make-Up

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Hassan Make-Up ya bayyana cewa, yana neman Afuwar duk wanda suka yi fada dashi ya yafe masa. Ya bayyana hakane yayin da yake kusa da ka'aba yake rokon dan darajar dakin Ka'aban duk wanda suka yi fada dashi ya yafe masa. A baya dai an ga Hassan Make-Up har kuka ya rika yi bayan da ya samu zuwa Aikin Umrah. https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7555127311583038776?_t=ZS-90A3JHC3sYq&_r=1
Kalli Bidiyo: Nima ga dana da Kachiya aka Haifeshi, Dan haka, Malam Lawal Triumph yayi daidai, Haihuwar mutum da Kachiya ba Karama bace>>Inji Malam Abdulhamid Dahir

Kalli Bidiyo: Nima ga dana da Kachiya aka Haifeshi, Dan haka, Malam Lawal Triumph yayi daidai, Haihuwar mutum da Kachiya ba Karama bace>>Inji Malam Abdulhamid Dahir

Duk Labarai
Malam Abdulhamid Dahir ya goyi bayan Sheikh Lawal Triumph kan kalaman da yayi cewa, Haihuwar mutum da Kachiya ba karama bane. Malam ya bayar da misali da dansa inda yace shima da Kachiya aka haifeshi dan haka, Haihuwar Mutum da Kachiya ba karama bace. Kalli Bidiyonsa a kasa: https://www.tiktok.com/@sheikh_lawan_triumph/video/7555274342100258055?_t=ZS-90A2h8MjRr7&_r=1
Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar rushe kungiyar PENGASSAN

Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar rushe kungiyar PENGASSAN

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar rushe kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta PENGASSAN. Yace idan kungiyar ta ci gaba da nuna son kai ba tare da la'akari da abubuwan da zasu kawowa al'umma ci gaba ba, ya kamata Gwamnatin tarayya ta soketa. Ranar Asabat, Kungiyar PENGASSAN ta fara yajin aiki bayan da ta zargi matatar man Dangote da korar membobin ta 800 daga aiki. A bangaren Dangote, yace Wannan yajin aiki PENGASSAN na son yin amfani dashine dan cimma wani buri nata na saka 'yan Najeriya cikin wahala. A hirar da aka yi dashi a Arise TV, Ndume yace baya goyon bayan Ayyukan kungiyoyin kwadago da suke daukar matakan biyan bukatarsu maimakon bukatar al'ummar Najeriya. Yace ina PENGASSAN take a lokacin da aka cire tallafin man fetur a Najeriy...
An tashi baram-baram a zaman sulhu da aka yi yunkurin yi tsakanin kungiyar PENGASSAN da Dangote

An tashi baram-baram a zaman sulhu da aka yi yunkurin yi tsakanin kungiyar PENGASSAN da Dangote

Duk Labarai
Rahotanni sun ce zaman sulhu da aka yi tsakanin wakilan kungiyar PENGASSAN da na Matatar Dangote an tashi ba tare da cimma matsaya ba. Gwamnatin tarayya ce ta kira zaman wanda aka fara ranar Litinin da misalin karfe 4 p.m.. Ministan kwadago, Mohammed Dingyadi da karamar ministan Kwadago, Nkiruka Onyejeocha sun halarci zaman wanda aka shafe awanni 9 ana yi. Minista Dingyadi yace za'a dawo ci gaba da zaman da misalin karfe 2 p.m. na ranar Talata. Gwamnatin tarayya tace tana duba abinda wannan rikici zai jawowa Najeriya ne shiyasa take kokarin sulhunta Bangarorin Dangote da PENGASSAN.