Tauraron me wakar Batsa, Soja Boy ya bayyana cewa, shekara me zuwa sai ya haihu ko ta halin yaya.
Ya wallafa hakan ne a shafinsa na Instagram.
Soja Boy yace ko da aure ko da cikin shegene sai ya dirkawa wata ta haifa masa yara.
Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, wani dan siyasa ya taba kai masa kudi cikin dare amma ya ki karba.
Malam ya bayyana hakane a wa'azin da yake yi wanda Bidiyon tuni ya dade da watsuwa a kafafen sada zumunta.
https://www.tiktok.com/@i.agashua001media/video/7551129407599971591?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7551129407599971591&source=h5_m×tamp=1758540663&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7545729042580113168&share_link_id=c92b3f5d-3cae-45...
Kashim Shettima Ya Isa Birnin New York Na Amurka Don Halartar Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Na 80 Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York domin halartar zaman taro na 80 na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda zai gudana daga ranar Litinin zuwa 28 ga watan Satumba.
An tarbe shi a filin jirgin sama na John F. Kennedy inda ya samu rakiyar ministoci da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar.
Shettima, wanda yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi a madadin Najeriya a taron, tare da halartar muhawarorin manyan shugabanni da kuma wasu tarurruka a gefen taron Majalisar.
Haka kuma, zai sanar da sabbin kudirin Najeriya na rage dumamar yanayi (NDCs) karkashin...
Wannan Sojar Najeriya ce dake kewar gida, tace shekarar ta guda bata je gida ba.
Sojar ta bayyana cewa a baya tana ganin kamar an tsaneta ana yawan sata wanke-wanke amma tace yanzu tana son zuwa dan ganin 'yan gidansu.
https://www.tiktok.com/@mercheeka/video/7552183080115588359?_t=ZS-8zw2L5wOhWa&_r=1
Gwamnan rikon kwarya na jihar River, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (retd.) Ya bayyana kin amincewa da binciken da majalisar jihar ke son yi masa.
Ya bayyana hakane bayan da majalisar jihar ta amince ta binciki watanni shida da yayi yana matsayin gwamnan jihar.
A ta bakin me magana da yawunsa, Hector Igbikiowubu, Ibas yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya nadashi kuma majalisar tarayya ta rika lura da aikin da yake.
Yace idan dai majalisar tace zata bincikeshi to tana son ta binciki shugaban kasar kenan da majalisar tarayya.
Saidai yace ba bu wanda zai hana majalisar jihar binciken idan tace tana son ta yi.
Bidiyon matashin me kudi, Saleem Goje yana yakin neman zabe a jihar Taraba ya dauki hankula.
An ga mutane na bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan shigarsa siyasa inda mafi yawanci suka nuna rashin jin dadinsu.
https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1969717740224094237?t=Cifm363nTsKT--TRIZcP6g&s=19
A ranar Juma'ar data gabata ne aka daura auren dan Sanata Abdulaziz Yari a Masallacin Sultan Bello Kaduna.
Shugaban Izala,Sheikh Bala Lau ne ya ya gabatar da huduba kamin zuwan liman.
Saidai a yayin da yake wa'azi, Alaramma Ahmad Sulaiman na ja masa baki, sai ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga masallacin.
Ai kuwa nan da nan Sheikh Bala lau ya janye lasifika daga bakin alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karatun Qur'anin ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu.
Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin bai kamata ba.
https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7552481590450900231?_t=ZS-8zvFbjBS0LA&_r=1
Dan babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, me suna Abdulrahaman Ahmad ya kammala makarantar horas da sojojin Najeriya, NDA.
Malam ya halarci wajan bikin yaye su da aka yi.
Wani fasto ya dauki hankula bayan da aka ga yana rabawa mata rigar mama.
Faston ya bayyana rashin jin dadinsa ne da ganin yanda mata ke zuwa cocin nasa babu rigar mama.
Dan hakane ya raba musu rigar maman amma yace ba zasu tafi da ita gida ba.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1969467628222661084?t=feabGIpcSzv_4kTqje1imw&s=19
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi gargadi cewa muddin 'yan Najeriya basu tashi tsaye ba suka yi abinda ya kamata a 2027 ba, to lallai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai so ya zarce ya mulki Najeriya har iya tsawon rayuwarsa.
El-Rufai ya kwatanta Abinda Tinubu ke son yi da irin mulkin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.
El-Rufai yayi wannan maganane a yayin da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai masa ziyarar jaje bayan tarwatsa taron ADC da aka yi a Kaduna.
El-Rufai yace ko mulkin Soja bai ga ana yin irin kamar karyar da Gwamnatin Tinubu ke yi ba
Dan haka yace dolene a hada kai.