Tuesday, December 16
Shadow

Duk Labarai

Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa ‘yansandan Jihohi

Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa ‘yansandan Jihohi

Duk Labarai
Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa 'yansandan jihohi. Kungiyar ta bayyana hakane bayan taro na masu ruwa da tsaki da ta yi a gidan shugabanta, Chief Reuben Fasoranti dake Akure. Ta yi kira ga shugaban kasar da ya fitar da kudirin doka wanda zai bayar da damar canja kundin tsarin mulkin Najeriya dan a samar da 'yansandan Jihohi inda tace ya aika da wannan kudirin dokar zuwa majalisa. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da sakataren yada labaran Kungiyar, Jare Ajayiya fitar inda yace sun yaba da kokarin Gwamnati na magance matsalar tsaro amma akwai bukatar a kara himma.
Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Duk Labarai
Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa. Gwamnatin Jihar Adamawa ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ta cire tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga sarautar Wazirin Adamawa. A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke bayyana cewa mutanen da ke masarautar su ne kaɗai ke da hakkin naɗa basarake da mambobin majalisar masarauta. Wannan sabon tsarin ya sa kafafen yada labarai da dama suka fassara cewa an cire Atiku daga matsayin Wazirin Adamawa. Amma a wani taron manema labarai da aka gudanar a jiya Laraba, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare na Jihar Adamawa, Iliya James, ya bayyana cewa wannan sabon tsarin bai cire kowa daga mukaminsa ba. Ya kuma ƙara da cewa duk wasu sabbin shirye-s...
2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa – Barau Jibrin

2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa – Barau Jibrin

Duk Labarai
2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa - Barau Jibrin. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa ko da yake ba ya son ya shiga cikin muhawarar wanda zai iya zama abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027, zai karɓi kowane nau’in aiki da Shugaban ƙasa zai danka masa cikin farin ciki da biyayya. Yayin wani taron manema labarai da aka shirya dangane da shirin jin ra’ayoyin jama’a a shiyyoyi daban-daban da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sauya Kundin Tsarin Mulki , Barau ya ce: “Duk abin da Shugaba ya bukace ni da in yi, zan yi shi dari bisa dari ” Wannan bayani na zuwa ne bayan wata magana da ya yi a ranar Talata, inda ya shawarci wata ƙungiya da ke goyon bayan kudurin sa ya zama mataimakin shugaban kasa a 202...
Kalli Hotuna: Yayin da shugaba Tinubu ke sanyawa dokar canja fasalin Haraji hannu

Kalli Hotuna: Yayin da shugaba Tinubu ke sanyawa dokar canja fasalin Haraji hannu

Duk Labarai
A yaune shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa dokar canja fasalin Haraji hannu. Shugaban ya sakawa dokar hannu a fadarsa wanda lamarin ya samu halartar kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da wasu gwamnoni da sauran manyan ma'aikatan Gwamnati. Sabuwar dokar harajin dai a cewar shugaban zata kawo ci gaba sosai a kasarnan har ga wadanda ba'a haifa ba.
Wallahi Ban taba sanin namiji ba, kuma za’a iya gwadawa a gani, mijin aure nake nema>>Budurwa ‘yar shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka

Wallahi Ban taba sanin namiji ba, kuma za’a iya gwadawa a gani, mijin aure nake nema>>Budurwa ‘yar shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka

Duk Labarai
Wata mata me shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka da cewa maza na gudunta suna cewa ta tsufa. Tace yawanci mazan dake zuwa wajanta mazan aurene kuma ba aure ke kaisu wajanta ba, suna nemanta da lalata ne. Tace da yawa idan suka ganta sai su ce ta tsufa. Ta koka da cewa ba ita kadai bace a wajan mahaifiyarta ba amma ita kadai ce bata yi aure ba. Matar tace wallahi bata taba sanin Namiji ba, kuma idan mutum na da yanda zai gwada, yana iya gwadawa ya gani. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita a wani gidan rediyo me suna Agidigbo FM inda tace tana neman taimakon a samo mata mijin aure.