Friday, March 6
Shadow

Duk Labarai

Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa

Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa

Duk Labarai
Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara. Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025. Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa'ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta SP Shi'isu Lawan Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya., Rundu...
Najeriya na shirin kwaso ‘yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya

Najeriya na shirin kwaso ‘yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya

Duk Labarai
Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida. Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar. Wata sanarwa da Ma'iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen. "An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui," a cewar sanarwar. "Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami'an tsaro a ranar Asabar."
EFCC ta tabbatar da daure Hamisu Breaker da Gfresh a gidan gyara hali saboda wulakanta Naira

EFCC ta tabbatar da daure Hamisu Breaker da Gfresh a gidan gyara hali saboda wulakanta Naira

Duk Labarai
Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFCC ta tabbatar da hukuncin daurin watanni 5 da akawa jarumin Tiktok, Gfresh da Mawaki, Hamisu Breaker saboda wulakanta takardar Naira. Hukumar tace duka su biyun bayan da aka karanto musu laifukansu sun amince basu yi gaddama ba. Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa. Cikin rahoton daEFCC ta fitar, kotun ta kama G Fresh da laifin "liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000" a...
Kalli Bidiyon yanda Wani Manomi ke gayawa shugaba Tinubu ba dadi bayan da ya kai masararsa kasuwa aka ce buhu dubu 20, yace ba zata yiyu ba

Kalli Bidiyon yanda Wani Manomi ke gayawa shugaba Tinubu ba dadi bayan da ya kai masararsa kasuwa aka ce buhu dubu 20, yace ba zata yiyu ba

Duk Labarai
Wani manoni ya bayyana rashin jin dadinsa bayan da ya kai masararsa kasuwa zai sayar aka ce masa Naira Dubu 20 duk buhu. manomin Yace wannan kudi ba zasu sai musu magani ko taki ba. Ya rika fadin hakan ba zata yiyu ba. https://www.tiktok.com/@opphicial_xelebrity/video/7530954943868439813?_t=ZM-8yKCWNQGzFm&_r=1
Ba gaskiya bane ikirarinka na cewa Tinubu ya ware Arewa wajan ayyukan ci gaba>>Gwamnatin Tarayya tawa kwanwaso martani

Ba gaskiya bane ikirarinka na cewa Tinubu ya ware Arewa wajan ayyukan ci gaba>>Gwamnatin Tarayya tawa kwanwaso martani

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta yiwa tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso martani kan ikirarin da yayi cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya watsar da yankin Arewa. Da yakewa Kwankwaso martani, Me magana da yawun shugaban kasar, Daniel Bwala yace Kwankwaso yayi kuskure. Shugaba Tinubu bai yi twasi da yankin Arewa ba. Daniel Bwala ya bayyana hakane a shafinsa na X inda ya zayyano irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi a Arewa. https://twitter.com/SundayDareSD/status/1948668988814180713?t=KoI-o8mAcldY5wqL-V-GMg&s=19
Gwamnatin tarayya ta kayyade shekaru 12 a matsayin shekarun shiga ajin karamar sakandare na JSS1

Gwamnatin tarayya ta kayyade shekaru 12 a matsayin shekarun shiga ajin karamar sakandare na JSS1

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta kayyade shekaru 12 a matsayin shekarun shiga ajin karamar sakandare na JSS1. Hakan na kunshene a bayanan da gwamnati ta fitar kan yanda makarantun kudi zasu riga gudanar da harkar ilimi. Sanarwar tace yaro sai ya kai shekara 3 sannan za'a sakashi a ajin Nursery 1 Sannan idan ya kai shekaru 4 a sakashi a ajin Nursery 2. Gwamnati tace kamin yaro ya fara ajin farko na primary watau Primary one sai ya kai shekaru 6. Dan haka kowane yaro sai ya kai shekaru 6 yana karatun Primary daidai lokacin da zai kammala Primary, ya zamana yana da shekaru 12. Dokar tace a daidai lokacin da yaro zai kammala sakandare zai kasance yana da shekaru 18 kenan.
Ga ‘Yan Najeriya na fama da yunwa, ga rikici tsakaninka da Kashim Shettima amma jam’iyyar mu ta ADC ce ta tsone maka ido>>Atiku ga Shugaba Tinubu

Ga ‘Yan Najeriya na fama da yunwa, ga rikici tsakaninka da Kashim Shettima amma jam’iyyar mu ta ADC ce ta tsone maka ido>>Atiku ga Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya mayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu martani kan sukar da shugaban kasar yayi ga jam'iyyar ADC. Shugaba Tinubu a wajan taron jam'iyyar APC inda aka zabi sabon shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa mutanen jam'iyyar ADC rikitattun mutanene. Saidai a martaninsa, Atiku yace akwai abubuwa da yawa da ya kamata Shugaba Tinubu ya mayar da hankali kansu maimakon sukar jam'iyyar ADC wanda ya mayar abin yi kullun. Yace tattalin arzikin Najeriya na cikin halin ni 'yasu, 'yan Najeriya na cikin yunwa, sannan ga rikici tsakaninshi da mataimakinsa, Kashim Shettima wadannan abubuwan ya kamata ya mayar da hankali kansu ba sukar jam'iyyar ADC ba.
Dan kudu zamu tsaida takarar shugaban kasa a 2027>>Inji Jam’iyyar PDP

Dan kudu zamu tsaida takarar shugaban kasa a 2027>>Inji Jam’iyyar PDP

Duk Labarai
Jam'iyyar PDP ta sanar da cewa, dan kudu zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2027. Jam'iyyar ta bayyana hakane a zaman masu ruwa da tsaki da ya wakana a jiya. Sannan ta canja wajan da zata gudanar da taronta na zaben shuwagabannin jam'iyyar wanda a da za'a yi a Kano, yanzu a jihar Oyo za'a yi. Ana zargin an yi hakanne dan shiryawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinda hanya a shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Saidai hakan kuma zai zama koma baya ga Nyesom Wike wanda tuni dangantaka tsakaninsa da Gwamna Makinde ta yi tsami.
Kalli Bidiyon: Yanda Shugaba Tinubu yayi subutar baki yace tsohon shugaban APC Dr. Rabiu Ganduje

Kalli Bidiyon: Yanda Shugaba Tinubu yayi subutar baki yace tsohon shugaban APC Dr. Rabiu Ganduje

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi subutar baki inda yace tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Rabiu Ganduje. Shugaban na son yace tsohon shugaban jam'iyyar APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne a wajan wani taro. Wasu dai Sun ce kwankwaso ne a ransa shiyasa. https://www.tiktok.com/@comr._aliyu_ak_balarabe/video/7530686949414276357?_t=ZM-8yJmcICu4iE&_r=1 Lamarin ya dauki hankula.