Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi

MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi

Duk Labarai
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJUUN. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi
Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus ya yin da wata gobara ta tashi da tsakar dare a kasuwar Terminus da ke birnin Jos na jihar Filato

Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus ya yin da wata gobara ta tashi da tsakar dare a kasuwar Terminus da ke birnin Jos na jihar Filato

Duk Labarai
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. An samu mummunar gobara da ta laƙume shagunan mutane da dama a babbar kasuwar Terminus a wani layi da ake ƙira da “Parlon Buhari” da ke Jos fadar gwamnatin jihar Filato a daren jiya. Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus a gobarar.
Ka sauka daga Gwamnan jihar Delta tunda a jam’iyyar mu aka zabeka>>PDP ta gayawa Gwamna Sheriff bayan a ya koma APC, ta garzaya kotu

Ka sauka daga Gwamnan jihar Delta tunda a jam’iyyar mu aka zabeka>>PDP ta gayawa Gwamna Sheriff bayan a ya koma APC, ta garzaya kotu

Duk Labarai
Jam'iyyar PDP ta yi martani kan komawar Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa jam'iyyar APC. Shugaban jam'iyyar na riko, Ambassador Umar Damagum, ya bayyana cewa sun tafi kotu da neman Gwamna Sheriff ya sauka daa kujerar Gwamna tunda a karkashin PDP aka zabeshi. Yace a baya sun fuskanci matsalolin da suka fi wannan yawa kuma duk sun tsallake dan haka wannan wasan yara ne. Yace an baiwa Gwamnatin gudanarwa na yankin kudu maso kudu umarnin ya kula da jam'iyyar PDP a jihar ta Delta saboda duka 'yan jam'iyyar a jihar sun canja sheka.
A dakin Otal Muka kama Nnamdi Kanu yana hutawa da wata mata>>Gwamnatin Tarayya

A dakin Otal Muka kama Nnamdi Kanu yana hutawa da wata mata>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
A ci gaba da shari'ar da ake tsakanin shugaban kungiyar dake son kafa kasar Biafra, IPOB, watau Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayya, Gwamnatin tarayya ta gabatar da shaidarta na farko. Lauyan Gwamnatin tarayya ya nemi shaidar ya rufe fuska saboda tsaro kuma Alkalin dake shari'ar ya amince da hakan hakana shima lauyan Nnamdi Kanu bai kalubalanci hakan ba. Shaidar ya bayyana fuska a rufe inda yace shine ya jagoranci jami'an tsaro zuwa dakin da Nnamdi Kanu yake a Otal. Ana zargin Nnamdi Kanu da cin amanar kasa, da aikata ayyukan ta'addanci.
Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta bayyana cewa, idan dai za'a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Hada kai da Atiku Abubakar ko El-Rufai kamin yayi nasara kada Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Mataimakin shugaban NLC ne ya bayyana hakan inda yace a zaben 2023, Peter Obi ya kama hanyar nasara kamin a samu tangardar da ta canja lamarin. Yace indai hukumar zabe me zaman kanta, INEC ba zata yi Magudi ba, to Peter Obi yana da karfin mabiyan da zai lashe zaben 2027.
EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano

EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano

Duk Labarai
EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano. Hukumar EFFC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano. BBC ta rawaito cewa, EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma'aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi. "Bayan bincike, jami'an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado," in ji EFCC cikin wata sanarwa. "An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta." Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma za ta kai su kotu da zarar an kammal...
Atiku Abubakar na shirin barin PDP

Atiku Abubakar na shirin barin PDP

Duk Labarai
Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 - all rights reserved Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa, Abokin takararsa Atiku Abubakar ma na shirin barin PDP. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Da aka tambayeshi ko ya sanar da Atiku maganar ficewarsa daga PDP Yace ya sanar dashi zasu yi zama na musamman dan nemawa kansu mafakar siyasa. Yace Atiku ma ya alamta cewa yana shirin barin jam'iyyar PDP.