Thursday, January 16
Shadow

Duk Labarai

Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Duk Labarai
Mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da komawar Tauraruwar Fina-finan Hausa, Asma'u Abdullahi Wakili zuwa jam'iyyar APC. Ya wallafa hakane a shafinsa na zada zumunta inda ya yi mata maraba zuwa jam'iyyar APC. https://twitter.com/barauijibrin/status/1854270065547329955?t=7dvUTEwRZF-CKrPmAxoNAQ&s=19 Asma Wakili dai Hadimace ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf saidai ta ajiye mukamin nata inda ta kuma fice daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC. Sanata Barau yace Asma Wakili ta sanar da ficewarta daga NNPP a yayin ziyarar data kai masa a Abuja. Barau ya kara da cewa Asma Wakili ta bayyana ayyukan alkhairi na jam'iyyar APC ne ya jawo ta zuwa jam'iyyar. Yayi kira a gareta data zama jakadiya ta gari ga Masana'antarta ta Kannywood, Jam'iyy...
Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial  Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana ra'ayinsa akan mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata da yawa ya kuma dauki Bidiyon faruwar lamarin. Sanata Sani yace Dalilin da yasa ake samun irin mutumin masu lalata da matan mutane a Ofis shine mata basu son mata 'yan uwansu su zama ogannin su. https://twitter.com/ShehuSani/status/1854454657164156931?t=Y3ueoL-V8O9o9aKXhIBBWw&s=19 Lamarin mutumin ya dauki hankula sosai inda akai ta Allah wadai dashi inda wasu suka rika yaba masa.
A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Dangote kotu inda suka ce su ba za su sayi Man fetur daga matatarshi ba dan haka ya kyalesu su siyo daga kasashen waje

A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Dangote kotu inda suka ce su ba za su sayi Man fetur daga matatarshi ba dan haka ya kyalesu su siyo daga kasashen waje

Duk Labarai
Manyan 'yan kasuwar man fetur su A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Aliko Dangote kotu inda suke bukatar kotu kada ta amince masa da bukatar da yayi na a hanasu siyo man fetur daga kasashen waje saidai su siya a hannunshi. Dangote dai ya shigar da 'yan kasuwar da NNPCL kotu inda yake neman kotun ta hana shigo da man fetur daga kasar waje a rika saya daga hannunsa. Dangote yace kawai ya kamata a shigo da man fetur Najeriya ne idan babu shi a matatarsa ko idan an samu karancinsa. Saidai su kuma 'yan kasuwar sun bayyana cewa Dagote na son ya zama shi kadai ne ke rike da harkar man a kasarnan wanda haka ba zai haifarwa kasuwar da mai ido ba. Sun ce idan aka baiwa Dangote wuka da nama na harkar zai zama shi kadai ne ke kayyade farashin wanda hakan bai k...
Sun gana mana Azaba sun barmu kwanaki 3 babu abinci>>Kananan Yara da Gwamnati ta kama bisa zargin yunkurin kifar da Gwamnati suka bayyana

Sun gana mana Azaba sun barmu kwanaki 3 babu abinci>>Kananan Yara da Gwamnati ta kama bisa zargin yunkurin kifar da Gwamnati suka bayyana

Duk Labarai
Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta kama a zanga-zangar tsadar rayuwar da aka yi sun magantu kan abinda ya faru. A hirar da jaridar Punch ta yi dasu, daya daga cikin wadanda suka fito daga Kano, Umar Ali me shekaru 15 ya bayyana abinda ya faru. Yace ba'a basu abinci yanda ya kamata wani lokacin sai da suka yi kwanaki 3 sannan aka basu abinci kuma abincin ba mai yawa ba gashi babu dadi. Umar Ali yace shi bai yi zanga-zangar ba ya fita ne zuwa wajan da yake aiki a Kwana Hudu dake Ungoggo inda a nan ne aka kamashi. Yace an ajiyesu a daki me duhu basa ganin rana, shiyasa bayan da aka fito dasu ko gani basa yi da kyau. Shima wani matashi me suna Ibrahim Aliyu Musa ya bayyana cewa an ajiyesu a guri daya da muggan masu laifi. Shima yace suna kwanaki da yawa babu abinci inda ya...
Mutane 2 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan fashewar bam a jihar Imo

Mutane 2 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan fashewar bam a jihar Imo

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Imo sun tabbatar da mutuwar mutane 2 bayan da bam ya fashe a kasuwar Orlu ranar Talata. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Henry Okoye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin jihar,Owerri. Yace mutane da yawa dake gudun neman tsira sun jikkata a harin inda yace suna kan bincike akan lamarin. Yace Wadanda suka mutu din wanda suka je saka bam dinne inda kamin su kammala sakashi ya tashi dasu. Kwamishinan 'Yansandan jihar, CP Aboki Danjuma ya aika da jami'an 'yansanda na musamman dake da kwarewa akan harkar bam wajan.
Zanga-zangar kin jinin Donald Trump ta barke a biranen kasar Amurka bayan da ya lashe zabe, Kalli Hotuna da Bidiyon yanda Amurkawa da yawa ke kuka saboda takaicin ya ci zabe

Zanga-zangar kin jinin Donald Trump ta barke a biranen kasar Amurka bayan da ya lashe zabe, Kalli Hotuna da Bidiyon yanda Amurkawa da yawa ke kuka saboda takaicin ya ci zabe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Amurkawa da yawa sun kwana da bakin ciki bayan da Donald Trump ya sake cin zabe a kasar a karo na biyu. Bidiyo da yawa sun bayyana inda suke nuna yanda Amurkawan ke takaici da mamakin cewa wai Donald ne ya sake cin zabe. Wasu an gansu suna kuka wasu suna takaici, wasu ma basu san abinda zasu yi ba. https://twitter.com/shellshockkk/status/1854184901496422697?t=FoTT9rOuJtM0QSZbdUPCMw&s=19 https://twitter.com/shellshockkk/status/1854148975600808396?t=TN8ZXWGMnSVJncqJsCL_BA&s=19 A hannu daya kum...
Me zai faru da shari’o’in da ake yi wa Trump bayan ya lashe zaɓe?

Me zai faru da shari’o’in da ake yi wa Trump bayan ya lashe zaɓe?

Duk Labarai
Bayan shafe makonni ana gwagwarmaya a yaƙin neman zaɓe, an ayyana Donald Trump na jam'iyyar Republican a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka. Tsohon shugaban ƙasar, shi ne na farko da aka samu da laifi, kuma zai kasance na farko da zai fara aiki yayin da ake ci gaba da sauraron shari'o'in laifuka da dama a kansa. Shigarsa ofishi mafi girma a Amurka yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume da dama ya jefa ƙasar cikin wani lamarin da ba a taɓa ganin irinsa ba. Ga abin da zai iya faruwa da ƙalubalen shari'a guda huɗu da yake fuskanta yayinda ya ke shirin komawa Fadar White House. Samunsa da laifin biyan kuɗin toshiyar baki a New York Tuni aka yanke wa Donald Trump hukunci kan laifuka 34 da suka haɗa da shirga karya kan bayanan kasuwanci a jihar New York. A watan...