Saturday, January 18
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

Duk Labarai
A shirye-shiryen bukukuwan karshen shekara, Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan titunan kasarnan. Hukumar dake kula da titunan Najeriya, FERMA ce dai ta ke kula da gyaran. Shugaban hukumar, Engr. Chukwuemeka Agbasi ne ya kaddamar da fara gyaran titunan a jihar Kano. Yace za'a yi wadannan kyaran ne dan samarwa mutane saukin ziyara da komawa garuruwansu dan yin bukukuwan karshen shekara. Yace sun gano titunan da aka fi amfani dasu kuma sune zasu fi baiwa fifiko a wajan gyaran. Ya bayyana cewa, wannan aiki zai samarwa da mutane akalla 12,000 abin yi wanda hakan zai habaka tattalin arzikin kasa.
Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu’a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga ‘yan Najeriya

Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu’a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Me Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na II ya yi kira ga 'yan Najeriya su daina tsinewa da kuma la'antar shuwagabanni inda yace su mayar da komai ga Allah. Yace 'yan kasa su rika yiwa shuwagabanni addu'a da ma kasar baki daya. Yace babu wani abu me kyau ko marar kyau dake dawwama,koma menene zai wuce kamar ba'a yi ba. Ya kuma jawo hankalin shuwagabanni dasu san cewa zasu tsaya a gaban Allah dan amsa yanda suka gudanar da mulki inda babu wanda zai karesu. Sannan yayi kira ga malamai da su rika gayawa mabiyansu gaskiya. Sarkin yayi wannan jawabine a wajan wani taro da ya gudana a Kaduna ranar Litinin inda aka hada malaman Addinin Musulunci da Kiristanci.
EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023, Efeanyi Okowa kan almundahanar Naira Tiriliyan 1.3

EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023, Efeanyi Okowa kan almundahanar Naira Tiriliyan 1.3

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa,EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Delta,Efeanyi Okowa akan zargin Almundahanar kudi. Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da Naira Tiriliyan 1.3. Kudin dai an bayyanasu a matsayin kaso 13 dinnan da ake warewa jihohin da ake hako man fetur a cikinsu. Wata majiya data san da lamarin tace an karkatar da kudadenne a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023. An kama Okowa ne a ranar Litinin a Birnin Fatakwal na jihar Rivers a yayin da ya je ofishin EFCC amsa gayyatar da suka masa. Hakanan ana kuma zargin tsohon gwamnan da karkatar da wasu kudaden na daban da suka kai Naira Biliyan 40

Tinubu Ya Himmatu Wajen Rage Raɗaɗin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki, Inji Minista

Duk Labarai
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar rage raɗaɗin da ‘yan Nijeriya ke ciki. Idris ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Kaduna a shirin ‘Hannu Da Yawa’ na Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Sashen Hausa. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana kan wahalar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, kuma ya ce tallafin yana amfanar wasu tsirarun mutane ne kawai. Ya ba da tabbacin cewa tattalin arzikin ƙasar nan zai daidaita, kuma babu wata gwamnati da za ta so a samu ci-baya a zamanin ta. Idris ya jaddada cewa abin da ya kamata a gyara a ƙasar nan ba ya ta’allaƙa ne ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wakilai da aka zaɓa ko kuma masu zartaswa na gwamnati kawai ba ne, ...
Ƴansanda sun gurfanar da masu zanga-zanga kan cin amanar ƙasa a jihar Borno

Ƴansanda sun gurfanar da masu zanga-zanga kan cin amanar ƙasa a jihar Borno

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Borno ta gurfanar da mutum 19 da suka haɗa da wasu ƙananan yara uku a gaban kotu bisa zargin hannunsu a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta. An gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Aisha Mohammed Ali a babbar kotun jihar da ke birnin Maiduguri a yau Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan ta janye tuhumar da ake yi wa ƙananan yara da aka kama saboda gudanar da zanga-zangar. A cewar takardar da aka gabatar a kotun, yaran uku suna tsakanin shekaru 14 zuwa 17. Gwamnatin jihar Borno ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da cin amanar ƙasa, da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen ɓat...
Da Duminsa: Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Da Duminsa: Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran da aka kama da zargin cin amanar ƙasa sakamakon shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa. Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kuma kafa wani kwamati da zai bincika yadda aka kama su da sauran lamurransu. "Shugaban ƙasa ya ce a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu," in ji ministan lokacin da yake magana manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Bayanan sun fito ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa a fadarsa a yau Litinin. Kwamatin da zai yi aikin zai kasance ƙarƙshin ma'aikatar agaji da rage talauci, in ji ministan.
Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu’a dan ta fita daga matsalar tsananin Rayuwa

Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu’a dan ta fita daga matsalar tsananin Rayuwa

Duk Labarai
Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu'a ta musamman domin neman sauƙin matsalolin da Najeriya ke fuskanta. Za a gudanar da addu'ar ne ƙarƙashin jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan ƙalubalen da suka yi ƙasar dabaibayi. Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu'ar ta ƙasa ne ya sanar da hakan a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ya ce akwai buƙatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalar da ƙasar ke fuskanta, inda ya nanata cewa haɗin kai na da muhimmanci wajen shawo kan dukkan matsala. "Bayan addu'ar, muna da yaƙinin Allah zai buɗe mana hanyoyin da za mu samu sauƙi," Afolo...
Farashin kayan Abinci zasu tashi a Najeriya saboda babu Network a bankuna

Farashin kayan Abinci zasu tashi a Najeriya saboda babu Network a bankuna

Duk Labarai
Matsalar rashin Network a bankunan Najeriya yasa ake tsammanin samun hauhawar farashin kayan abinci. Manyan jiragen ruwa sun kawo abunci kala-kala daga kasashen waje inda suke gabar tekun Legas suna jira a kammala duk takardunsu na haraji wadanda suka makale a bankuna saboda matsalar rashin Network. Rahoton daga jaridar Naigerian Tribune yace kayan auna kan ruwa inda masu kayan suke jiran takardunsu, inda matsalar take shine duk kwana daya da kayan suka kara sai mai kaya ya sake biyan kudin haya na Kwantena da kayansa suke ciki. Wakilin masu kawo kayan Mr. Frank Ogunojemite ya bayyana cewa, suna bukatar gwamnati ta rika basu wani dauki ko tallafi a irin wannan yanayi saboda ba laifinsu bane. Yace duka kudin hayar da suka biyawa kayan nasu akan wanda zasu sayi kayan zasu fanshe...
Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Duk Labarai
Wannan mutumin wanda dan kasuwane dan kasar Equatorial Guinea ya shiga idon duniya bayan da bidiyo sama da guda 400 suka bayyana inda suka nunashi yana lalata da mata. Wani abin karin ban mamakin shine cikin matan da yayi lalata dasu hadda matan aure da kuma matan manyan 'yansiyasa na kasar. Rahotanni sun ce cikin matan manyan mutanen da yayi lalata dasu akwai matar ministan shari'a na kasar, da matan sauran ministoci. Akwai kuma matar kaninsa. Da matar kawunsa. Da matar Faston cocin da yake halarta. Da matar uban gidansa. Da matar me tsaron lafiyarsa. Da abokan kanwarsa da dai sauransu. Rahoton yace mutumin baya amfani da kwandam wajan yin lalata da matan. Tuni dai an garzaya dashi kotu inda kotun tace a je a gwadashi ko yana dauke da cutar dake yaduwa ta...
Mu talakawa ne ba za mu iya yin belin yaranmu ba – Iyayen yaran da aka tsare

Mu talakawa ne ba za mu iya yin belin yaranmu ba – Iyayen yaran da aka tsare

Duk Labarai
Iyalan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga a Kano da Kaduna sun koka kan a yi masu adalci. Iyaye da ƴan uwan yaran sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa yaran su basu da hannu kan zargin da ake masu na cin amanar ƙasa, inda suka roƙi hukumomi da su sakar masu ƴaƴansu. Mutanen sun bayyyana cewa su talakawa ne basu da ƙarfin da za su cika dukkan sharuddan beli da kotu ta bayar a Abuja. An kama masu zanga-zangar 76 a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa daga ɗaya zuwa 10 ga watan Agusta, inda aka gurfanar da su a gaban babbar kotun Abuja a ranar Juma'a. Al'umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar. Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyan...