Saturday, January 18
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Yanda wata Daliba a kasar Iran ta tube kayanta, ta yi Tumbur, haihuwar uwarta a tsakiyar makaranta saboda an mata hukunci kan shigar banza da ta yi

Kalli Bidiyo: Yanda wata Daliba a kasar Iran ta tube kayanta, ta yi Tumbur, haihuwar uwarta a tsakiyar makaranta saboda an mata hukunci kan shigar banza da ta yi

Duk Labarai
Wata daliba a jami'ar Tehran’s Science and Research University dake kasar Iran ta dauki hankalin Duniya saboda tabarar da ta yi. Sanin kowane kasar Iran kasar Musulunci ce da bata wasa idan mata suka yi shigar banza ana hukuntasu sosai. Wannan dalibar hukunci ya hau kanta inda jami'an tabbatar da da'ar dalibai na jami'ar Tehran’s Science and Research University suka hukuntata saboda shigar banza da ta yo ta je makarantar. Saidai abin bai mata dadi ba inda kuwa nan take ta cire kayanta gaba daya daga ita sai rigar mama sai dan kamfai watau Pant. Ta rika cire pant dinta tana nuna Al'aurarta watau irin abinnan dai dake nuna cewa in kashe ta za'a yi saidai a kasheta gashi ma ta yi tsirara gaba daya haihuwar uwarta. Tuni dai aka kamata aka tafi da ita zuwa asibitin mahaukata dan ...
Dattawan Yarbawa sun ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan fifiko da yake nunawa wajan baiwa Yarbawa mukamai da yawa fiye da sauran kabilun kasarna

Dattawan Yarbawa sun ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan fifiko da yake nunawa wajan baiwa Yarbawa mukamai da yawa fiye da sauran kabilun kasarna

Duk Labarai
Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan yawan baiwa yarbawa mukami a gwamnatinsa fiye da sauran kabilun kasarnan Sanatarwar hakan ta fito ne daga shugaban kungiyar da kuma da kuma sakataren yada labaranta Ayo Adebanjo, da Justice Faleye. Kungiyar tace fifikon da Tinubu ke nunawa ka iya bata dangantakar dake tsakanin Yarbawa da sauran kabilun kasarnan. Sun kuma jaddada cewa dolene Tinubu ya gyara wannan kuskure da yayi. Kungiyar tace ba zata kwashe shekaru tana Adawa da irin wannan lamari ba a mulkin sauran shuwagabanni wanda ba yarbawa ba amma a shugabancin bayerabe ta yi shiru ba. Kungiyar dai tace duk shuwagabannin EFCC, CBN,DSS, Army, Navy, 'Yansanda, Customs, Immigration, Bank of Industry, Babban Lauyan Gwamnati, Alkalin A...
Kasar Libya na kama ‘yan Najeriya dake zaune a kasar da kakaba musu haraji me yawa saboda Haushin Najeriya da suke ji kan wasan kwallon kafa da basu yi nasara ba

Kasar Libya na kama ‘yan Najeriya dake zaune a kasar da kakaba musu haraji me yawa saboda Haushin Najeriya da suke ji kan wasan kwallon kafa da basu yi nasara ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Libya na cewa hukumomi a kasar na yiwa 'yan Najeriya dake zaune a kasar kamun kan mai uwa da wabi da kakaba musu haraji me yawa dan Huce haushi. Najeriya dai ta yi nasara akan kasar Libya ne bayan da Najeriyar ta kai karar kasar Libya kan cin zarafin da tawa 'yan wasan Super Eagles. Hukumar kwallon kafa ta Africa CAF ta baiwa Najeriya gaskiya inda ta baiwa Najeriya maki 3 sannan ta ci kasar Libya tarar Dala $50,000. Najeriya dai ta je kasar Libya ne dan buga wasa zagaye na biyu na neman shiga gasar cin kofin nahiyar Africa. Saidai hukumomi a kasar ta Libya sun karkatar da jirgin 'yan wasan Najeriyar zuwa wani gari na daban dake da nisa da wajan da za'a yi wasan. Hakanan an ki baiwa 'yan wasan Najeriyar motar da zata kaisu garin da zasu yi wasan kuma Gw...
Ko kunsan cewa kotu tace a ci gaba da tsare yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan za’a ci gaba da shari’ar su?

Ko kunsan cewa kotu tace a ci gaba da tsare yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan za’a ci gaba da shari’ar su?

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa ta bayar da umarnin a kaisu gidan yari a ci gaba da tsaresu har sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan a ci gaba da shari'a. Saidai a wani sabin rahoto da hutudole ya samu, babban lauyan Gwamnati ya bukaci a mayar da maganar shari'ar yaran ofishinsa inda kuma ya nemi a dawo da ranar ci gaba da shari'ar kusa. A wata majiya daga ma'aikatar shari'ar tace ana tsammanin nan da ranar Talata me zuwa za'a iya dawowa a ci gaba da shari'ar sannan kuma gwamnati na shirin janye zargin da takewa yaran.
Wata Sabuwa: Wasu daga cikin yaran da gwamnatin tarayya ta kama take zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu sun bace an rasa inda suka shiga

Wata Sabuwa: Wasu daga cikin yaran da gwamnatin tarayya ta kama take zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu sun bace an rasa inda suka shiga

Duk Labarai
Daya daga cikin lauyoyin dake baiwa yaran da gwammatin tarayya ta kama bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga watau Deji Adeyanju ya bayyana cewa, basu san inda yara 2 daga cikin yaran da gwamnatin tarayyar ta kama auke ba. Yace yaran biyun ya kamata ace an gurfanar dasu a gaban kotu tare da sauran yara 32 da aka kai kotu ranar Juma'ar data gabata. Saidai yace zuwa yanzu basu san inda yaran suke ba kuma basu san abinda ya faru dasu ba. Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punch ta yi dashi.
A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

Duk Labarai
Babban lauyan gwamnati kuma ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ya fara shirin janye karar da gwamnatin tarayya ta shigar akan kananan yara na cewa aun ci amanar kasa ta hanyar yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga. Awanni bayan da aka gurfanar da yaran su 32 dai Lauyan Gwamnatin ya bayyana bukatar karbar shari'ar daga hannun 'yansanda. Yace akwai abubuwan da suke son sake dubawa game da shari'ar. Kotu ta dai bayyana cewa sai ranar 1 ga watan Janairu sannan za'a ci gaba da wannan Shari'a inda ta tura yaran zuwa gidan yari. Saidai babban lauyan gwamnatin yace ya nemi a canja ranar ci gaba da wannan Shari'ar watau a matso da ita kusa. Wata majiya daga ma'aikatar Shari'a ta bayyanawa jaridar Punch cewa tuni shugaban 'yansanda ya mikawa babban lauyan gwam...

Allah Sarki, Gwanin Ban Tausai, Kalli Bidiyon yanda aka mayar da kananan yara ‘yan Arewa cikin motar gidan yari za’a kai a ci gaba da tsaresu bayan da suka kasa biyan Naira Miliyan 10 kudin beli

Duk Labarai
Bayan kammala zaman kotu da aka yi da kananan yaran nan 'yan Arewa da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ta gurfanar a gaban kotu, an sake mayar dasu gidan yari. An ga yaran sunata rokon a taimaka musu a yayin da aka kullesu a cikin motar gidan yari za'a tafi dasu. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1852715208873005392?t=8s_f8EHSbdItxi1u3a_8Lw&s=19 Lauya me basu kariya, Deji Adeyanju ne ya tsaya yake basu baki akan lamarin.
Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari’a

Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari’a

Duk Labarai
Babban lauya,Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da gwamnatin Tinubu ta gabatar a gaban kotun tarayya dake Abuja a kotu bisa zargin cin amanar kasa. Femi Falana wanda lauyane na kare hakkin bil'adama ya bayyana cewa kotun bata da hurumin tuhumar yaran. Yace kotun ta gaggauta sakinsu sannan kuma gwamnati ta dauki nauyin karatunsu akalla zuwa sakandare ko jami'a. Yace ko da sun aikata laifi, ba tare da manyan mutane za'a yanke musu hukunci ba dolene a kaisu inda ake yankewa yara hukunci.
Bazan taba bayar da kudi dan yiwa mutane auren gata a mazabata ba saboda bana son ganin karin yara da yawa>>Inji Dan majalisar Tarayya, Bello El-Rufai

Bazan taba bayar da kudi dan yiwa mutane auren gata a mazabata ba saboda bana son ganin karin yara da yawa>>Inji Dan majalisar Tarayya, Bello El-Rufai

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai ta tarayya kuma da a wajan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana cewa ba zai taba biyan kudi a yiwa mutane auren gata a mazabarsa ba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yo dashi wadda hutudole ya bibiya. Yace dalilinsa kuwa baya son ganin karin yawan yara. Yace a yanzu haka a Arewa yawanmu ya wuce kima amma kuma bamu da isashshen ilimi. https://twitter.com/IU_Wakilii/status/1852740532964855995?t=ZXKaUEF7mQX2zUghhpdiIg&s=19 Lamarin yawa da almajirci na kananan yara dai a bayyane yake a Arewacin Najeriya.
Allah Sarki kalli bidiyon yawabi me sosa Zuciya na Sheik Makari akan Kananan yaran da gwamnatin Tinubu ta kai Kotu

Allah Sarki kalli bidiyon yawabi me sosa Zuciya na Sheik Makari akan Kananan yaran da gwamnatin Tinubu ta kai Kotu

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama kuma Limamin masallacin Abuja, Sheikh Makari ya bayyana takaici da kama yaran da gwamnatin Tinubu ta yi ta kai kotu da sunan sun ci amanar kasa. Babban malamin yace babu inda ake irin haka a Duniya. Yace zasu dauki nauyin kula da yaran kamin a sakosu sannan kanana daga ciki zasu dauki nauyin karatunsu. https://twitter.com/Realoilsheikh/status/1852706767139946625?t=5MbxAjpwwcIeKYmpbOe1mQ&s=19 Malamin ya bayyana a wani faifan bidiyo ne a wajan karatu inda aka jishi yana jawabin