Wata Sabuwa: Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu bisa zargin cin amanar kasa na iya fuskantar hukuncin kìsà
Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin kisa na daga cikin hukuncin da kananan yara da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu a Abuja zasu iya fuskanta.
Yaran dake da shekaru 14 zuwa 17 su 29 ko 32 a wasu rahotannin sun baiwa mutane tausa yi sosai bayan ganinsu cikin tashin hankali,yunwa da rashin lafiya.
Yaran sun rika yanke jiki suna faduwa saboda yunwa bayan da aka gabatar dasu a kotu, saidai Hukumar 'yansandan Najeriya tace duk karya suke kawai dan su jawo cece-kuce ne.
Saidai duk wanda ya ga yaran yasan suna cikin tashin hankali dan idanuwansu sun yi zuru-zuru ga kasusuwan hakarkarinsu duk a waje ga jikinsu ba alamar kuzari duk dai alamun yunwa sun bayyana a tattare dasu.
Rahoton VOA yace yaran zasu iya fuskantar hukuncin kisa saboda shine hukuncin laifin cin amanar kasa da ake z...