Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa 'yan Najeriya miliyan 24 tallafi daban daban da suka hada dana bashi dana koya sana'a da dai sauransu.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai.
Ya kara da cewa tallafin da suka bayar sun hada da bangaren Noma, Makamashi, masana'antu kiwon lafiya da dai sauransu.
Hakan na zuwane a yayin da 'yan Najeriya ke ta fama da kokawa da matsin tattalin arziki wanda yasa kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi.