Wednesday, March 11
Shadow

Duk Labarai

An kubutar da yara 4 da aka sace daga jihar Bauchi aka kaisu Jihar Anambra aka sayar

An kubutar da yara 4 da aka sace daga jihar Bauchi aka kaisu Jihar Anambra aka sayar

Duk Labarai
Hukumar 'yansanda a jihar Anambra ta sanar da kubutar da wasu yara 4 da aka sato daga jihar Bauchi aka kaisu Anambra aka sayar dasu ga wasu iyalai. Kwamishinan 'yansandan jihar, Obono Itam ne ya bayyana haka inda yace sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a lamarin. Ya hayyana hakane ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda yake bayani game da yanda hukumar tasa ta gudanar da ayyukanta a shekarar 2024. Yace daya daga cikin yaran an ganeshi kuma dukansu za'a mayar dasu ga iyayensu. Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.
‘Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam’iyyar siyasa’

‘Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam’iyyar siyasa’

Duk Labarai
Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) wadda wasu ƴan siyasa daga arewacin Najeriya suka kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam'iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027. Ƙungiyar ta zargi jam'iyya mai mulki ta APC da babbar jam'iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Naeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar. A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar. Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas. Sai dai tuni jam'iyyar APC ta mayar da ma...
Dattawan Arewa sun koka da kwamitin da aka kafa domin duba ƙudurin haraji

Dattawan Arewa sun koka da kwamitin da aka kafa domin duba ƙudurin haraji

Duk Labarai
Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta koka kan rashin shigar da ƙwararu a kwamitin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci ofishin ministan shari’a da na majalisar ƙasar su kafa domin sake duba ƙudurorin cikin tsanaki. Ƙungiyar ta ce bai kamata gwamanti ta nemi a kawo sauye-sauye cikin gaggawa kan batun dokar harajin ba, inda ta ce aiwatar da dokar ba tare da tuntuɓa yadda ya kamata ba zai yi wa jihohin yankin illa. Farfesa Abubakar Jika Jiddere ɗaya ne daga cikin shugabanin ƙungiyar ya ce kawo yanzu sun kamala yi wa dokar harajin duba na tsanaki kuma sun haɗa rahotonsu, wanda haka yasa suke ganin dole a sake nazari kan ƙudurin.
‘Yansandan Abuja sun kama mutum 50 da zargin sace murafen kwatami

‘Yansandan Abuja sun kama mutum 50 da zargin sace murafen kwatami

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen binrin Abuja ta ce ta kama mutum 50 da take zargi da ɓallewa tare da sace murafe na kwatami a kan titunan birnin. Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukan zumunta ta ce tsararren samame da ta kai ne ya ba ta nasarar kama mutanen, inda kuma dakarunta suka ƙwato murafe 25. Birnin na Abuja ya daɗe yana fama da waɗannan sace-sace, inda ake yawan cire murafen da ke tsakiya ko gefen titi domin sayarwa. "Bincike ya tabbatar cewa masu satar na aiki ne a matsayin wani gungu da ke sayar da murafen ga dillalan ƙarafa," in ji sanarwar wadda ta lissafo sunayen mutum 50 ɗin. Daga cikin abubuwan da ta ce ta ƙwace a hannun mutanen har da turakun lantarki masu amfani da hasken rana na gefen titi, da ababen hawa uku, da rodin gina gadodji, da sauran abub...
EFCC ta kori ma’aikatanta 27 saboda ‘zambatar’ mutane

EFCC ta kori ma’aikatanta 27 saboda ‘zambatar’ mutane

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta kori ma'aikatanta 27 a shekarar 2024 saboda zargin aikata zamba da sauran laifuka. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya amince da matakin. "Duk wani zargi da aka yi wa wani ma'aikacin hukumar, sai an bincika shi, ciki har da na dala 400,000 da ake yi wa wani ma'aikaci da ba a gano shi ba zuwa yanzu," a cewar sanarwar. Ya ƙara da cewa EFCC "na sane da ayyukan sojan gona da ɓata sunan da wasu ke yi da ta hanyar amfani da sunan shugaba [Olukoyede] domin zambatar manyan mutanen da ake zargi", wanda shi ma ake kan bincikawa.
Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

Duk Labarai
Matsanancin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙasar Saudiyya. Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi a cikin garin Makka. Haka kuma an ga yadda wasu maza suka riƙe da hannu domin ceto yaran da suka maƙale sanadin ambliyar ruwan a unguwar Al-Awali. Sai da aka soke jigilar wasu jiragen sama a birnin Jeddah, inda aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo hukumomin Saudiyya suka rufe makarantu a daukacin ƙasar.
Bam ya kashe mutum biyu a wata Islamiyya a Abuja

Bam ya kashe mutum biyu a wata Islamiyya a Abuja

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce wani abin fashewa ya kashe mutum biyu a makarantar Islamiyya da ke Abuja babban binrin ƙasar. Wata sanarwa da rundundar ta wallafa ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Litinin a ƙauyen Kuchibuyi da ke ƙaramar hukumar Bwari. "Bayanan farko-farko sun nuna wasu mutum uku ne suka kai wa shugaban makarantar Tsangayar Sani Uthman Islamiyya Mallam Adamu Ashimu ziyara, kuma su ake zargi da kai bam ɗin," in ji sanarwar. "Biyu daga cikin mutanen sun mutu a fashewar a farfajiyar makarantar, yayin da na ukun da kuma wata mata mai sayar da kayayyaki suka ji munanan raunika kuma suke samun kulawa a asibiti." Sanarwar ta ƙara da cewa 'yansanda na tsare da Mallam Adamu, sannan kuma za ta bayyana abin da bincikenta ya gano.
Kalli Bidiyo da Hotuna: Kungiyar B0k0 Hàràm ta kaiwa Sansanin Sojojin Najariya hari ta kashe sojoji 7

Kalli Bidiyo da Hotuna: Kungiyar B0k0 Hàràm ta kaiwa Sansanin Sojojin Najariya hari ta kashe sojoji 7

Duk Labarai
Kungiyar ISWAP data balle daga jikin B0K0 Hàràm ta kaiwa sansanin sojojin Najariya hari a garin Damboa dake jihar Borno. Maharan sun kona gidaje da motocin sojojin da kashe akalla sojoji 7. Rahoton Sahara Reporters yace maharan sun shafe awanni 2 suna cin karensu ba babbaka a sansanin sojojin. Rahoton yace harin ya farune ranar 4 ga watan Janairu, watau Asabar data gabata. Wani soja yace zuwa yanzu sun gano gawarwakin Sojoji 7, kuma ya kara da cewa an kai musu harinne da misalin karfe 4 na safe. Kalli Bidiyon anan
Sojoji sun mamaye garin Shinkafi saboda barazanar Bello Turji

Sojoji sun mamaye garin Shinkafi saboda barazanar Bello Turji

Duk Labarai
Kwanaki kadan bayan da gawurtaccen dan ta'adda, Bello Turji ya kaiwa wasu unguwannin garin shikafi hari, sojoji sun mamaye garin dan samar da tsaro. Yaran Bello Turji sun kai hari a kasuwar garin inda suka Kashe mutane 2 da yin garkuwa da wasu da dama. Turji dama yayi Alkawarin kaiwa garin Shinkafi hari idan ba'a saki wasu 'yan uwansa da aka kama ba. Turji ya kuma tare motoci biyu ya yi garkuwa da mutanen ciki ya koma mota daya.