Ƴansanda sun kama wata mata bisa zargin kàshè kishiyarta a Bauchi, bayan ta kkàsheta, ta kuma watsa mata ruwan zafi sannan ta tattara buhu ta cinnawa gawar wuta
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed kan zargin kashe kishiyar mai suna Hajara Isa hanyar shaƙeta a gidan mijinsu.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, Ahmed Wakil ya fitar ranar Talata ya ce tuni rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Ya ce mijin matan - Sale Isa - ne ya kai ƙorafi wajen ƴansanda a ranar Talata.
Wakil ya ce bayan fara gudanar da bincike ƴansanda suka kama matar mai suna Fatima Mohammed mai shekara 28, wadda daga baya ta amsa laifinta a lokacin ƴansanda suke tuhumarta.
“A lokacin da ake tuhumarta ta amsa laifinta inda tace shaƙe kishiyartata ta yi, har sai da ta mutu'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ''bayan ta kashe ta, ta yi ƙoƙarin yin ɓadda-bami, ta yadda ba ...








