Wata Sabuwa: Jafar Jafar yace Mutuminnan da ya yi ikirarin shi dan kasuwane ya baiwa Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu me babban Shago kyautar Mota da Shago a Sokoto, Ashe dansanda ne
A jiyane, Hutudole ya kawo muku rahoton yanda wani dan kasuwa ya baiwa Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu kyautar Mota da shago a jihar Sokoto.
Rahama ta nuna Bidiyon yanda aka bata kyautar a shafinta na Tiktok.
Saidai a wani Rahoto da mawallafin jaridar Daily Nigerian Jafar-jafar ya wallafa yace wannan mutumin dansanda ne.
Ya kuma ce bai kamata a samu Dansanda da irin wannan hali ba.
Saidai yace watakila yana wakilatar wanine.
https://twitter.com/i/status/2020213730999439635








