‘Muna fargabar barkewar cutuka masu muni a Maiduguri’
Masana harkokin lafiya a Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta aike da tawagar likitoci na musmaman da suka kware kan cututuka masu yaɗuwa zuwa Borno saboda fargabar barkewar cututuka sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta a jihar.
Masanan sun ce, suna fargabar barkewar cututuka irinsu zazzabin cizon sauro, da Zika, da zazzabin typoid, da na dange, da kuma uwa uba amai da gudawa, sakamakon irin dattin da ambaliyar ruwa ta kwaso da gawarwakin makabartu da ruwan ya dauko.
Dr Nasiru Sani Gwarzo, babban sakataren ma'aikatar Ilimi a Najeriya, kuma masani kan harkokin kiwon lafiya ya shaida wa BBC cewa, dole ne hukumomi su gaggauta shawo kan ruwan da ya malale asibitin koyarwa na Maiduguri saboda wasu daga cikin na'urorin asibitin akwai wadan ke da sinadarin nukiliya a ciki da k...







