An yi jana’izar mutanen da harin jirgi ya kashe bisa kuskure a Zamfara
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun ce an yi jana'izar 'yan aikin sa kai da wani jirgin yaƙi da ake zargin na sojojiin Najeriya ya kai musu hari bisa kuskure a ƙauyen Tungar Kara.
Wani mazaunin ƙuyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana'aizar 'yan sa kan su 17 da suka mutu a harin, yayin da wasu ke kwance a asibiti.
A ranar Asabar da maraice ne wani jirgi da ake kyautata zaton na sojin ƙasar ne ya kai hari bisa kuskure kan 'yan sa kai a ƙauyen na Tungar Kara.
Lamarin ya auku ne, yayin da suke ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.
Wani mutum - da ya rasa ɗan'uwansa a harin, ya bayyana wa BBC cewa ƴan sa kai da dama ne lamarin ya rutsa da su yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan ...








