Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji – NLC
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji da ya gabatar ga majalisar dokokin ƙasar domin bayar da dama kan sake yin nazari.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a yau Laraba.
Saƙon ya ce “domin samar da tsarin dimokuraɗiyya mai tabbatar da ci gaban ƙasa, dole ne mu gina tsari kan tubalin tattaunawa, da bai wa masu ruwa da tsaki damar tsoma baki a harkar gina ƙasa.
“A kan haka ne muke sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta janye ƙudurin harajin da yanzu haka ke a gaban Majalisar dokoki domin bai wa duk ɓangarorin da suka dace bayar da gudumawa a kansa”.
Sanarwar ta ce ƙungiyar, ita ma za ta so ta taimaka wajen samar da kyakkyawan tsarin haraji wanda zai ...








